TARIHIN SAYYADINA UMAR ƊAN KHAƊƊABI RALIYALLAHU ANHU (KASHI NA DAYA)
Sayyadina Umar Ɗan Khaɗɗabi Raliyallahu Anhu
Sunansa da Asalinsa
Sunansa Umar ɗan Khaɗɗabi ɗan Nufail ɗan Abdul Uzza ɗan Rayahi ɗan Abdullahi ɗan Ƙurɗi ɗan Razahi ɗan Adiyyu ɗan Ka’abu ɗan Lu’ayyu ɗan Galibu al Adawi al Ƙurashi. Ya haɗu da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a zumunci ta wajen kakansa na takwas Ka’abu ɗan Lu’ayyu wanda shi ne kakan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na bakwai.
Mahaifiyarsa ita ce ƙanwar Abu Jahli, Hantamah ɗiyar Hisham ɗan Mughirah daga ƙabilar Makhzum.
Haifuwarsa:
An haifi Sayyiduna Umar bayan yaƙin nan da aka fi sani da Harbul Fijar a shekara ta Arba’in da uku kafin hijira. Don haka Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya girme shi da shekaru goma cif.
Siffarsa Da Ɗabi’unsa:
An siffanta Umar da cewa, mutum ne dogo, kakkaura, mai sanƙo a kansa. Ga shi kuma jawur yake kamar ƙwara. Saboda tsawonsa idan ka hango shi daga nesa za ka yi tsammanin mahayi ne.
Game da ɗabi’unsa kuwa, Umar ya gaji kaushin hali daga mahaifinsa. A lokacin ƙuruciyarsa ya kasance yana yi wa mahaifin nasa kiyon raƙuma. Mahaifin kuwa yana wahalar da shi sosai, yana kuma dukansa idan ya saɓa masa.
Mahaifin Umar, al Khaɗɗabi ya kasance yana wahalar da ƙanensa Zaidu musamman ma lokacin da ƙanen nasa ya ƙyamaci bautar gumaka, ya je neman addinin gaskiya na Annabi Ibrahim. Shi kuma Umar ya kan wahalar da ɗan baffansa kuma mijin ƙanwarsa Sa’idu ɗan Zaid, musamman a lokacin da ya san ya musulunta tare da matarsa.
Rayuwarsa Kafin Zuwan Musulunci
Muna iya raba rayuwar Sayyiduna Umar gida biyu; kashi na farko ya yi shi kafin zuwan Musulunci, kashi na biyu kuma a cikin Musulunci. A kashi na farko na rayuwarsa, Umar bai zamo wani mutum mai cikakken muhimmanci ba, duk da yake yana cikin ‘yan majalisa. Amma furta kalmar shahadarsa ke da wuya sai ya koma wani muhimmin mutum wanda rayuwarsa take da muhimmin ambato daga wannan rana har zuwa ranar tashin ƙiyama.
Umar shi ne wakilin ƙabilarsa ta Banu Adiyyin a majalisar zartaswa ta ƙuraishawa wadda ta ke da kujeru goma kamar yadda muka faɗa a baya. Kuma ofis ɗinsa shi ke kula da hulɗar ƙuraishawa da sauran ƙabilu musamman ga abin da ya shafi yaƙi da sulhu da makamantansu kamar yadda ya gabata a tarihin Abubakar.