AureSoyayya

Yadda Zaku Morewa Soyayyar Ku


Masoya da dama suna shiga kunci soyayya ne saboda rashin sanin yadda zasu morewa soyayyar su.


Wannan darasin zai koyawa masoya yadda za su yi soyayya cikin farin ciki.

Idan kuna so ku maorewa soyayyar ku to ku tabbatar da cewar kuna da kyankywan sadarwa a tsakaninku.


Sadarwa tsalanin masoya yanada mahimmanci sosai. Domin ta hakan ne masoya zasu morewa soyayyar su.
Duk wasu masoyan da suke burin son su more soyayyar su, dole ne ya zama suna samun lokaci a junasu.


Soyayya ba zai yiwu ba muddin masoya basa baiwa juna lokacin su.
Karfafawa juna wani hanya ne na maorewa soyayya.


Muddin masoya zasu zamto suna kushe kudirin juna, to zasu samu matsala.
Yafewa juna kurakure ga masoya abune dake karfafa soyayya.


Idan masoya zasu zama masu riko ko yawan mita akan kurakurensu. Bazasu morewa soyayyar su ba.


Kada masoya su zama masu kushe da rashin nunawa juna godiya idan sunyiwa juna abun kirki.


Idan namiji yayi abun yabo yanada kyau macen ta nuna masa hakan ta hanyar nuna godiyanta. Haka ma namiji idan mace tayi abu na gari ya yaba mata.


Kada masoya su zama marasa yiwa juna barkonci. Ana so aga masoya tamkar abokai suna wasa dariya ta hanyar nishadantar da junansu. Hakan na sa soyayya ya yi inganci.


Idan masoya suka yiwa juna laifi dole ne wanda yayi laifin ya fito ya bada hakuri tare da rarrashin wanda aka batawa. Wannan na sa masoya su morewa soyayyar su.


Bawai namiji ne kadai zai yi ta yiwa waccs ake soyayya da ita hidima shi kadai ba. Yana da kyau ita ma macen ta rika samun wani lokaci tana yiwa maisonta kyauta ta hanyar saya masa kyautukan da zai yi amfani dasu.

See also  Yadda Zaki Rage Zubar Ni'imar Gabanki


Idan masoya zasu zama masu tausayawa juna tun kamin aurensu zasu morewa soyayyar su.


Kada ya zama cewa babu ruwan su da matsalolin su. Idan mace nada matsala namiji yayi kokarin ganin ya taimaka mata daidai karfinsa. Ita ma mace ta nuna raahin jin dadinta da nunawa mai sonta da tana da halin taimakwa da tayi ba kawai ta barshi shi kadai yayi ta kunci ba.

Babu shakka muddin masoya zasu shigo da wadannan abubuwan a tsarin soyayyar su, babu tantama zasu morewa soyayyar su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button