Waec

Cikakken Tarihin hukumar Waec

An kirkiri Hukumar WAEC ne A lokacin da akayi wani Taro Kan Makomar ilimi a kasashen “Yammacin AFIRKA” Wanda yahada wakilan Makarantu da dama, daga cikin wakilan Makarantun da suka halarci wannan tattaunawa Akwai :-


1- Wakili daga University of Cambridge Local Examinations Syndicate.


2- Sannan Akwai wakili daga University of London School Examinations Matriculation Council


3- Sannan akwai wakili daga West African Departments of Education.


Sunyi taronne a Shekarar 1948, Inda suka tattauna akan makomar ilimin Yammacin Afirka.


Inda Suka kira taron da Suna “Tattaunawa kan makomar ilimi a kasashen Yammacin Afirka”


A karshen taronne ma kuma suka nada Dr. George Barker Jeffery( Wanda Darakta ne a University Of London Institute Of Education, a wancan lokacin) a matsayin Wanda zai ziyarci wasu daga cikin Kasashen Afirka, domin yaganewa idonsa halin da ilimi yake ciki a kasashen, tareda Samar da rahoto akan hakan.


Inda ‘Jeffery’ yakai ziyara ta tsawon, wata uku daga (watan Disambar 1949 zuwa watan March na Shekarar 1950),

Kasashen da ya ziyarta sun hadar da Kasar Ghana, Gambia, Sierra Leone, dakuma Kasar Najeriya,


Inda bayan kammala ziyarar tasane ya bada rahoton cewa ana buqatar kafa Hukumar “West African Examination Council”,


Bayan Amincewar gwamnatocin, Kasashen sai aka kafa Hukumar Jarrabawar ta “West African Examination council”


Inda aka fara gudanar da jarrabawar a Wasu daga cikin Kasashe, kamar haka:-

•Najeriya

•Ghana

• Sierra Leone

•Da kuma kasar Gambia,

Anfara Gudanar da jarrabawarne a watan Disambar Shekarar 1951.A Wannan shekarar Kasar Laberiya takasa cika sharuddan da’aka gindaya, inda hakan yakawo tasgaro a gudanar da jarrabawar a Kasar, inda sai a Shekarar 1974 aka fara gudanar da jarrabawar a Kasar ta Laberiya .
• TARON HUKUMAR NA FARKO

Bayan kafa Hukumar , an kira taro na farko a Accra, Babban Birnin Kasar Ghana a watan March na Shekarar 1953,


Wanda a taronne aka kafa kwamitoci guda 5, don su dinga taimaka wa Hukumar.Kwamitocin da aka kafa sune:-

1.Administrative and Finance Committee

2.School Examinations Committee

3. Public Service Examinations Committee

4.The Professional, Technical and Commercial Examinations Committee

5.Local Committee.


Mutane 26 ne suka halarci wannan taron na farko da aka gudanar a Kasar Ghana.


Ga sunayensu:-


1.Mr. A. N Galsworthy (Shugaban Hukumar)

2. George Barker Jeffery(Chief Secretary of the West African Inter-Territorial Secretariat)

3.Mr. J. L. Brereton (Secretary of the Cambridge Syndicate)

4. membobi 13 da gomnatocin Najeriya, Ghana, Sierra Leone, da Gambia, suka zaba.

5.Sai mutane 10 daga kasashen turai.

BIKIN CIKAR HUKUMAR SHEKARU 50 DA KAFUWA:-


A shekarar 2002 ne, Hukumar ta WAEC Tayi bikin cika shekaru hamsin (50th anniversary) da kafuwa, Wanda aka gudanar da Bikin a Abuja, Babban Birnin Kasar Najeriya,


Inda Aka sanyawa taron suna “WAEC: 50 years of Excellence”.


Dukkan membobin kasashen West Africa sun Halarci bikin a Abuja.

A Lokacin bikin ne aka kaddamar da Littafin
“The West African Examinations Council (1952-2002): Half a century of Commitment to Excellence and Regional Cooperation”.


Dafatan kun Amfana da wannan Tarihi na Hukumar WAEC.Nagode


Naku A ko da yaushe: Miftahu Ahmad Panda.


Muna fatan zaku kasance tare da wannan shafi domin samun Sahihan Bayanai akan Harkokin Ilimi dakuma sauran Muhimman Batutuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button