Abdul-Hadi Isah Ibrahim.

Tazarar dake tsakanin Me Kudi da Talaka

Marubuci: Abdul-Hadee Isah Ibraheem.


Akwai wata magana me girma da Allah
Madaukakin Sarki yayi a cikin Al-Qur’ani game da Economy, tattalin arzikin da zaman lafiyar mutane, a cikin Surah ta 59 (Suratul Hashr) a Ayah ta 7, wannan maganar da ace za’a tsaya ayi ta a aikace (Practically) da babu wanda zai zo yana kuka ya rasa me zai ci bayan Musulunci ya kafu, shekaru samar da 1,400 da suka wuce, wannan magana da Allah yayi tana da karfin gaske, Allah yace:

ما أفاء الله على رسوله من أهل القرى فلله وللرسول ولذي القربى واليتامى والمساكين وابن السبيل كي لا يكون دولة بين الأغنياء منكم وما آتاكم الرسول فخذوه وما نهاكم عنه فانتهوا واتقوا الله إن الله شديد العقاب

Ba fassara Ayar zanyi ba, sai dai Point din da nake so kawai zan Ciro daga cikin ta. Ayar tana magana ne game da duniyar da Allah ya azurta Manzon Allah dashi wajen karban Dukiyoyin Mushirikai, da wadanda aka karbo ba tare da an Gwabza yaki ba da sauran Kudaden da Allah yake bayarwa Gwamnatocin Musulunci da su kansu Musulmi, Allah yace za ayi amfani da kudaden ta bangarori kamar haka:

1. Aiki wa Musulunci.
2. Kula da hidimar Manzon Allah.
3. Da makusanta (wasu Malaman suka ce Salaries ne na Ma’aikatan Gwamnati, Fansho da Gratuity da sauran Grants).
4. Kula da Marayu.
5. Da Miskinai da Talakawa (wadanda za ayi musu Social investment program, ana biyan su wasu kudade Koda su ba Ma’aikatan Gwamnati bane, kamar N-POWER ko SURE-P kenan nake bada misali dasu son mu fahimci abun sosai).
6. Matafiyi wanda Kudin sa ya kare a hanya.

~ Daga karshe bayan Allah ya zayyano wadannan abubuwa sai yace anyi muku wannan tsarin ne domin kowa ya dinga samun kudi da abinda zai rayu cikin kwanciyar hankali ba tare da an bude Kofar da Kudaden zasu dinga zagayawa a tsakanin masu Kudin kadai ba, ba tare da Talakawa suna amfana ba, ku lura, Allah yace:
كي لا يكون دولة بين الأغنياء منكم

A shekarar 2021, NBS wato “National Bereau of Statistics” ta fitar da wani Nazari dake nuna cewa kaso 40 cikin ‘darin ‘yan Nigeria basa iya kashe Naira dubu 137,430 a duk shekara.
~ Wannan yana nuna maka yadda tazara, Gibi da nisan dake tsakanin the Rich and the poor, yayin da a Kasashe irin su Ghana zaka samu 40 percent din sune wadanda suke iya kashe Naira dubu 807,000 a shekara…
Talakawan da suke komawa su zama masu Kudi ‘yan kadan ne akan masu Kudin da suka kara yin Kudi a kullum.

~ Ka tsaya kayi tsam da ranka zaka ga kudade da Dukiyoyi suna yawo ne a tsakanin masu Kudi kadai, a nan kasar mu kenan muke magana. Gwamnati Koda zata cire Kudi zaka ga ba zai shafi talakawan Kai tsaye ba, wannan kuma shine tushen karyewar duk wata ‘kasa.
~ Idan ka lura da Ayar nan zaka ga cewa Allah ya shigo da wadanda suka fi yawa a cikin mutane, sune talakawa, da kuma dukkan wadanda idan Kudi bai kai gare su ba toh zasu tagayyara, tagayyarar su kuma idan an kaisu Bango zai yi illa wa rayuwar kowa da kowa, maganin matsalar kawai abi tsarin da idan an kasa kowa zai samu.

A nan Nigeria kusan kullum nisan tana ‘kara yawa, masu Kudi suna Kara kudancewa, talakawa suna ‘kara talaucewa.
The rich gets richer and the poor become poorer. Wannan ba karamin hatsari bane ga tsaron kasar, da zaman lafiyar kasar, shiyasa tun tuni Al-Qur’ani ya rushe Aqidar Communisanci, saboda Aqida ce da babu Rahama da tausayi acikin ta.

~ Wancan Ayar da Allah yayi magana akan cewa duniya ta dinga zagayawa tsakanin jama’a wannan shine asalin Economic Security, shine Food Security da duk wani Security da ake neman a duniya.
~ So, muna jan hankalin hukumomi suyi gaggawan gyara wannan matsalar domin idan Me Kudi yana ‘kara yin Kudi talaka baya matsawa gaba toh karshe kasar ba zata zaunu ba, ba zata mulku ba. Rike Dukiyoyin kasa da na jihohi ba’a sakin su ga talakawa suna samun abin yi lallai zai sabbaba abinda Allah baya so a cikin wancar Ayar☝️ shine Bad Revolution against the true leadership.

Idan ka kalli Theories irin na su Karl Marx, a cikin babban Theory dinsa na “The theory of immiseration” zaka ga kusan gaba daya kishiyar wannan Ayar yake kokarin nunawa da tabbatar da Aqidar Communisancin da ya yarda da ita na kasar sa ta Jamus.
~ Duk da cewa akwai wasu ‘yan abubuwa masu kyau a theory din, amma a Musulunce zaka ga kuma akwai shirme masu yawan gaske.

Babu wani tsarin Poverty Eradication a duniya kamar tsarin da Allah ya kafa na Zakka, da yadda ake fitar da ita.
Zakka is a Devine instructions game da kawar da talauci a duniyar Musulmi, but a yau Musulmi kamar sunfi kowa kukan talauci da matsalar rashin Kudi.
~ In sha Allah zamu samu lokaci muyi magana akan Zakka da yadda Allah ya tsara ta don ta kawar da talauci daga Musulmi masu Imani su rayu cikin wadata da arziki.

Wancan Gap dake kara fadi tsakanin talaka da me Kudi a kullum yana illa ga kowace kasa, saboda Kudi basa juyawa suna shiga hannun talakawa, Kudade su dinga fitowa daga masu Kudi da Gwamnati suna shiga hannun talakawa shine babban manufar wancan Aya da muke magana akan ta, idan ba haka ba toh babu wani abinda zai tafi dai dai a kasa idan ba Agogo ba, shima kafin Batir dinsa yayi sanyi.

~ Manzon Allah yace “Abinda ya halakar da wadanda suke kafin ku shine Rowa”.
Kin fitar da Kudade don talaka ya amfana, masu Kudi sun rike, Gwamnati ta rike, sai kasashen su suka lalace, shine halakar da suka yi, shugabanci ya gagara, bad revolution against the true leadership ya tabbata.
~ So, lallai muna kira a duba wannan lamari.
Allah yasa mu dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button