Nasir I. Mahuta

KO DON WANNAN DALILIN YA ISA A CIRE TALLAFIN MAN FETUR.A rubutun da ya gabata Corruption and Smuggling shi ne dalili na karshe da na zayyano a matsayin dalilan da sa ya kamata a kashe tallafin man fetur kafin tallafin man fetur ya kashe mu. Amma na dawo da shi lamba ta biyu ne domin tambayoyin da ake yi. Kafin mu yi nisa wajen bayani akwai bukatar mu san yadda ake shigo da mai a Nigeria.

Lamarin shigo da mai da kuma tallafin mai wani abu ne da ke a sarkake kuma da wahalar fahimta amma bari na yi kokarin fito maka da kadan daga yadda abin ya ke.

Hukumar NNPC ita ce ke da alhakin shigo da mai Nigeria tare da rarraba shi zuwa lungu da sako na nigeria. Sannan ita ce ake ba wa kudin tallafin mai din da ake biya domin Yan Nigeria su sayi fetur da arha. NNPC na shigo da fetur ne da kanta tare da kuma wasu kamfanoni da ba zan iya zayyano maka adadinsu ba. Kadan daga ciki akwai; Aiteo Group, Oando Plc, Forte Oil Plc, Total Nigeria Plc, A.A. Rano and Oil and Gas Ltd, A.Y.M. Shaffa da sauran kamfanonin mai da yawa a Nigeria.

Kamfanonin na shigo da fetur ta hanyar bin matakai uku:

1. Procurement and Shipment: Bayan samun sahalewar gwamnati wajen ba su damar shigo da man fetur, kamfanonin na kulla alaka da manyan kamfanonin mai na kasashen wajen ko matatun mai na kasashen waje wajen sayo mai daga gare su tare da kawowa tashoshin mai na Nigeria.
2. Customs Clearance: Da zarar fetur din da su ka sayo ya iso, jami’an customs za su duba fetur din tare da ba su Izinin karasowa da shi cikin Nigeria.
3. Storage and Distribution: Mafi yawan kamfanonin suna da gurin da su ke tara mai dinsu (depot) da zarar sun shigo da fetur depot dinsu ko na NNPC su ke kaiwa su aje, wanda daga nan ne kuma ake rarraba man zuwa lungu da sako na Nigeria.

Wadanda kamfanoni su ne ake ba wa tallafin man fetur din da ake magana. Suna gabatar da INVOICE na farashin yadda su ka sayo mai din da kuma adadin yadda su ka sawo ga NNPC, ita kuma NNPC sai ta ba su kudin tallafin akan kowacce lita da su ka sayo domin a sayar da mai din cikin sauki a Nigeria.

Mai karatu ka dai ji kadan daga yadda ake shigo da fetur da kuma yadda ake biyan kudin tallafin mai. Yanzun kuma bari mu yi bayanin yadda cin hanci ke shigowa cikin lamarin. A binciken da na gudanar, na fahimci almundahana na shigowa harkar tallafin mai ta hanyoyi kamar haka:

Shell Companies: Akwai zage-zage masu karfi kan cewa kamfanin Shell na da kamfanoni da yawa da ke da sunaye daban daban a fadin duniya. Idan mai karatu bai manta ba kamfanin Shell na daga cikin kamfanonin da ke fitar da crude oil daga Nigeria domin sayarwa a kasashen waje, sannan kuma kamfanin still yana sayo fetur daga kasashen waje zuwa Nigeria. To akwai zargi akan cewa kamfanin Shell yana daukar crude oil na Nigeria tare da sayarwa kansa da kansa ta hanyar sayarwa kamfani mallakarsa, tare da sayo fetur daga kamfanonin ya kawo nigeria. Ma’ana dai kamfanin ke sayarwa kansa crude oil kuma ya sayarwa Nigeria fetur a ba shi tallafi. Wannan bayani ne mai zurfin gaske zan takaita iya nan. Idan zargin ya tabbata gaskiya hakan na nufin kamfanin shell zai iya manipulating na adadin mai din da ya fitar tare da adadin fetur din da ya sawo. Tunda kamfanin na iya fitar da Crude oil zuwa kasashen waje ya sayar, kuma a kasashen wajen kamfanin na nan a matsayin sunansa na Shell ko a wani sunan daban. Kamfanin zai iya fitar da barrel na crude oil misali 100,000 a matsayin barrel 60,000, kuma ya sayo lita 100 million na fetur a rubu ce alhalin kuma iya lita million 50 ya shigo da shi. Yana da damar hakan, saboda shi ke sayarwa kansa kuma ya sayo daga kansa ya samu ribar sayarwa da sayowa kenan bayan ribar karbar tallafin man fetur din da ya wuce adadin da ya kawo na hakika.

1. Fake Importation Claims: Ba iya kamfanin Shell kadai ba, hatta sauran kamfanonin da ke iya shigo da mai a Nigeria ana zarginsu da yin takardun bogi da ke nuna sun kawo mai don su karbi tallafi ko kuma su chanja adadin yawan fetur din da su ka shigo da shi su karbi tallafin da ya wuce na adadin man da suka shigo da shi Nigeria.

2. Collusion with Officials: Ta hanyar amfani da jami’an Gwamnati, akwai zargin ana tafka almundahana. Misali, customs da ke clearance na adadin mai din da aka shigo da shi a yi amfani da su wajen bayar da shedar an shigo da mai alhalin ba’a shigo da shi ba ko kuma kara yawan adadin da aka shigo da shi akan adadi na gaskiya. Amfani da ma’aikata wajen biyan kudin fetur din da ba a shigo ba, tare da ha’intar adadin kudin da aka biya na tallafin mai din ma. Akwai zage-zagen cewa akan hada kai da jami’an NNPC a cike takardun bogi na cewa an biya tallafin da ba a biya ba.

3. Diversion and Smuggling: Akwai rade-radin cewa kamfanonin da ke shigo da fetur da sauran kamfanin da ke sayar da fetur ana Nigeria suna daukar man da aka biya wa tallafi su kai kasashen makafta kamar Benin, Niger, Cameroon da Chad su sayar a farashi mai tsada. Ma’ana mai din da Gwamnatin ta biya wa tallafi ana daukar shi ana kai wa wasu kasashen ana sayarwa a farashi mai tsada. Ka ga kenan kamfanonin sun samu kudin tallafi sannan sun samu ribar sayarwa a wasu kasashen.

Lamarin smuggling na fetur ba boyayyen abu ba ne domin kusan duk kasashen da na lissafa da ake kai man Nigeria na ziyarce su kuma na ganewa kaina yadda tankunan man nigeria ke shigar da mai zuwa kasashen. Shi ya sa a nawa hasashen 40% na man da ake biya wa tallafi ba a Nigeria ake sayar da shi ba a kasashen waje ake sayarwa. Ah to ga dan karamin misali, duk lokacin da aka kara kudin fetur a Nigeria ka bincika kasashen nan sai ka ji su ma mai ya karu.

Mai karatu, Wallahi kadan na gutsuro maka akan badakalar da ake yi da tallafin man fetur. Kada ka manta a rubutuna da ya gabata na yi bayanin yadda kudin da ake biya da sunan subsidy ya ke cinye kusan rabin kudaden da nigeria ke samu. To duk da hakan fa almundahana ake zabgawa wajen karkatar da kudin.

Cire tallafin man fetur zai sanya Gwamnati ta daina biyan kudin mai din da ba a kawo ba aka rubuta an kawo a takarda. Zai sanya ta daina biyan kudin tallafi na adadin mai din da bai kai adadin da aka kawo ba amma aka ce an kawo. Zai sanya ta daina biyan tallafin fetur din da ake sayarwa wasu kasashen da ke makaftaka da mu. Abinda zai ba ka mamaki shi ne, Nigeria na sayo fetur daga Niger a ba wa kamfanonin da suka sawo tallafi, kuma su sake maida mai din Niger su sayar a farashin da suka sawo. Ba iya Niger kadai ba, kasashe da yawa hakan na faruwa.

See also  HALAYE 8 DA ZASU KAIKA ZUWA GA SAMUN NASARA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button