Aure

Mafi Sauki Yadda Zaki Nunawa Namiji Rashin Amincewarki


Akwai matan da suke jin nauyin su fito fili su nunawa namijin daya nuna yana sonsu basa sonsa. Wasu kuwa wajen nuna masa ko furta masa kalmar basa so, babu hikima ko hankali a yin hakan. Wannan yasa wasu matan suke haduwa da fushin wasu mazan da har suke musu asirai.


Ka wasu hanyoyin da zaki iya nunawa namiji kina sonsa ba tare da kin cutar da shi ba.

1: Rashin Amsa Wayarsa: Idan har namijin da baki so ya samu lambarki kuma ya dameki da kira, kada ki rika daukar lambarsa.


Duk kuwa da wasu maza suna da naci, kina dauka sai ki bashi hakuri ki nuna masa kina wani uzuri ne. Idan ya sake kira kada ki dauka.


Wannan hanya ce da namiji mai hankali zai fahimci cewa bai samu shiga ba.


2: Sakon Text: Duk wani sakon da zai tura miki na text, whatsapp, inbox DM a takaice, kada ki amsa masa ko guda. Asali ma kiyi kamar baki gani ba.


Duk namiji mai natsuwa daya ga mace na masa hakan, ya tabbatar da cewa bai samu shiga bane zai ja jikinsa.


3: Kada Ki Tsaya Dashi Na Tsawon Lokaci: Namijin da baki so zai iya tsayar dake idan kun hadu a wani wajen. Kada kice bazaki tsaya ba. Kada ki bashi hankalinki idan kin tsaya, kada ki amsa masa tambayoyinsa kai tsaye idan ya miki.


A kullum namiji yana son ganin cewa mace ta tattara hankalinta waje guda ne idan yana magana da ita.

Yana son samun hadin kan mace na bashi bayanan da yake nema daga gareta. Muddin ya rasa wadannan abubuwan a wajen macen daya gani yana so, zai iya hakura ganin bai samu shiga ba.

See also  Yadda Zaki Rage Zubar Ni'imar Gabanki


4: Kada Ki Amince Da Kyautarsa: Duk yadda kike kin namij, muddin zai miki kyauta sai ya samu galaba a kanki koda kuwa ba aurenki zai yi ba.


Babban alama da namiji yake iya fahimtar mace batason sa shine na kin amimcewa ta karbi wani kyauta na bajinta da yayi mata.


Idan namiji zai ciro mudi masu yawa ya baki yaga kin ki karba, ko ya miki sayayya yaga kince baki bukatansu, nan take zai fahimci bai samu shiga ba zai iya hakura.


5: Rashin Bashi Dama: Idan har baki son namiji kada ki bashi damar da zaki rika amfani da umurninsa.


Akwai namijin da zai ce zai rage miki hanya, ko zai saukeki a unguwa. Ko zai warware miki wata matsalar da kike ciki. Ko zai taimaka miki a wani abunda kika kasa yinsa ko samunsa. Muddin zaki bashi dama a irin wadannan abunuwan to kina bashi dama ne da zai ci gaba da damumki da sunan soyayya.

Babban kuskure ne mace ta fito gatsau ta nunawa namiji bata sonsa. Kiyi amfani da alamun da zai fahimta ko za a fahimtar dashi bai samu shiga ba maimakon yin tsageranci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button