Tech

Menene Affiliate Marketing, da kuma yadda ake fara shi?

AFFILIATE MARKETING MAGANI A GONAR YARO;

Content Program:
1.MENENE AFFILIATE MARKETING?

2.YAYA AFFILIATE MARKETING YAKE?

3.ME AKE BUƘATA DOMIN FARA AFFILIATE MARKETING?

4.MENENE AFFILIATE LINK?

5.TAYA MUTUM ZEYI AFFILIATE MARKETING?

5.DA WANNE KAMFANI YA KAMATA A FARA?

a ko yaushe in ana maganar samun kuɗi ta yanar gizo akan yawan faɗin kalmar affiliation Marketing a baki amma dayawa basu taɓa Jarrabawa bama ko fahimtar yaya haƙiƙanin abun yake.

MENENE AFFILIATE MARKETING?

Kai tsaye tsari ne na shiga tsakanin mai siya da mai siyarwa ko mai aiki da wanda za’a yiwa aiki tsakanin kamfanoni da ma’aikatu tsakanin mutum da mutum wato “refer a friend to earn a money”

Affiliate Marketing ɗaya ne daga cikin dabarun talla na zamani da Manyan kamfanoni da ƙanana suke amfani dashi domin cimma burin samun sababbin abokan hulɗa a ko ina a faɗin duniya.

YAYA AFFILIATE MARKETING YAKE?

Yadda Tsarin yake kamfanin ne zasu tsara tsararren tsarin Affiliate Marketing ɗinsu wato hanyar yin rijista Da kuma tsarin biya; misali kamfanin zaice zakayi Rijista amatsayin Affiliate Marketer Kuma zai baka Affiliate Link Wanda dashi ne zakayi amfani wajen tallan kayayyakin sa ko ayyuka sannan zai faɗa maka duk kaya ɗaya da aka siya ta hanyar tallan ka(Affiliate Link Ɗin ka) zai biya ka adadin kuɗi kaza (slated amount) Kuma ta hanyar wannan Link Ɗin ne za’a gane cewa wannan customer Ɗin Daya siya wannan kayan ta hanyar ka ne sannan kuma kamfanin zai tsara hanyar biyan ka misali ta PayPal ne kokuma ta wasu hanyoyin biyan kuɗi ne kokuma direct transfer ne dss.

Abun fahimta shine Affiliate Marketing talla ne na zamani kamar misali kamfani yace yana siyar da kayayyakin sa duk mutum ɗaya da ka kawo yasiya zai baka 5% na kuɗin wannan tsarin shine yake taimakawa kamfanoni tallata kasuwancin su cikin sauƙi Abunda ake cewa “free ads startup”

See also  Yadda ake tura Hoto, Video, Waƙa ko kuma wani file a matsayin document ta whatsapp

ME AKE BUƘATA DOMIN FARA AFFILIATE MARKETING?

Ba wani kayan gabas bane abubuwan da ake buƙata sune kamar haka:
Wayar Android ko computer

Social media account/blog

Mabiya dayawa a shafukan sada zumunta

Iya tsara Ads content

Sanin kamfanin da daza’ayi Affiliate Marketing dashi.

Yadda za’a Fara Affiliate Marketing; kai tsaye da zaran Mutum ya zaɓi kamfanin da yakeso yayi Affiliate Marketing dasu sai yaje website ɗinsu yayi Rijista amatsayin Affiliate ko associate Rijistar tanada sauƙi kawai ana buƙatar email ne, full name, full address, Phone Number dss personal information.

Bayan kammala rijista kamfanin zasu tuntuɓe ka irin kayayyakin su ko services ɗinsu da ka zaɓi tallata musu anan dole ne mutum ya zaɓi ɓangaren daya san al’ummar dayake rayuwa acikin su suna buƙatar irin wannan kayayyakin ko services ɗin SBD sauƙin samun siyarwa dazaran angama zaɓar category shikenan kamfanin zasu bawa mutum Affiliate Link.

MENENE AFFILIATE LINK?

Affiliate Link shine link Ɗin da za’a bawa mutum na ɓangaren kayayyakin da ya zaɓi tallan su ko services Kuma link Ɗin is a unique wato nashi ne nashi kaɗai Wanda Shine zai dinga nuna cewa kaine kayi tallan Kayan idan an siya ta hanyar wannan Link Ɗin ne za’a ƙididdige adadin mutanen da suka Duba kayayyakin a tallan dakayi Dakuma Wanda suka siya kuma ta hanyar sa ne za’a biya mutum kuɗin sa na Affiliate Marketing Ɗin.

TAYA MUTUM ZEYI AFFILIATE MARKETING?

Abune me sauƙi eh! Ƙwarai dagaske wannan Link Ɗin (Affiliate Link) da’aka bawa mutum shine zai yi amfani dashi wajen sanyawa a blog ɗinsa, ko shafin ko page ɗinsa ko group ɗinsa har a WHATSAPP ma wato yadda mutum zeyi zai tsara Content ɗinsa ne akan wannan Product Ɗin ko services ta hanyar tallatawa daga ƙarshe sai yace ga link Nan game buƙatar siya ko buƙatar irin wannan aikin.

See also  AMFANI DA NA'URAR "P.O.S" LOKACIN CIRAR KUDI

Shin ana Samun kuɗi a Affiliate Marketing?

Eh! Ƙwarai dagaske gwargwadon ƙoƙarin mutum da yawan mabiyan sa gwargwadon samun sa har ila yau ƙwarewar mutum a Content creation tana taka muhimmiyar rawa wajen samar da kuɗaɗe masu tarin yawa.

Da wanne kamfani Yakamata a fara Affiliate Marketing?

Kusan kowanne Global marketplace suna Affiliate Marketing saide kowanne da irin tsarin su kaɗan daga cikin misalin dazan bayar sune:

Jumia Affiliate Marketing
Konga affiliate marketing
Amazon Associate
Alibaba express affiliate marketing
GoDaddy affiliate program
Da dukkan Manyan marketplace da sauran tech. Companies na duniya.

Muma a kamfanin ALBADAR muna gab da fara tsarin affiliate marketing.
ISMA’IL ALIYU UBALE
https://t.me/fasaharalbadar
Albadar Global Agency Ltd
WhatsApp 08086251045
22nd February 2023

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button