TARIHIN ABU UBAIDAH IBN AL-JARRAH, عامر بن عبدالله بن الجراح;
cikakken suna Abū ‘ubaydah’ Amir dan ‘Abdullāh dan al-Jarah ( Larabci 583-66 CE), yana daga cikin Sahabban annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama. Mafi yawa da aka sani da kasancewa ɗaya daga cikin wandanda aka yiwa alkawarin Aljanna. Ya kasance kwamandan babban runduna ta rundunonin Islam na kasar sham a lokacin Halifa Umar ( RA ) kuma yana cikin jerin Gwamnonin da Umar ya nada a matsayin Khalifanci. yana daya daga cikin wandanda suka amshi Musulumci tun daga farkon da’awar Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata agareshi. ya halacci yake-yaken Musulunci.
An haifi Abu Ubaidah a shekara ta 583 Miladiyya a gidan ‘Abdullah bn al-Jarrah, dan kasuwa mai sana’a. Abu Ubaidah asalinsa Qurayshu ne daga Banu al-Harith bn Fihr. Kafin ya musulunta, an dauke shi daya daga cikin mashahuran Quraishawa kuma ya shahara a cikin Quraysh na Makka saboda girman kai da jaruntakarsa.
Shiga Musulunci.
A shekara ta 611, Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama yayi kira zuga tauhidi ,tauhidin Allah ga mutanen Makkah. Ya fara kira ne da kiran mafi kusancita da sahabbansa da dangi sa a asirce zuwa ga addinin Musulunci shi LAA ILAHA ILALLAHU MUHAMMADUN RASULULLAHI cewa BABU WANI ABUN BAUTA FACE ALLAH KUMA ANNABI MUHAMMADU MANZON ALLAH NE. Ya musulunta kwana daya bayan Musuntar Sayyaduna Abubakar ( RA ) a shekara ta 611 yana dan shekara 28
Hijira zuwa Abiyasina/Habasha/Ethiopia.
Abu Ubaidah ya rayu cikin mummunan yanayin da musulmi suka shiga ciki a Makka tun daga farko har karshe. Tare da sauran musulmi na farko, ya jure wulakanci da zalunci na Quraishawa. Kamar yadda hijira ta farko zuwa Abiyasina ( Habasha ) ta yi nasara, wannan cin zarafin da aka yi wa musulmai ya yi nasara sosai.
Hijira zuwa Madina.
A cikin 623 Miladiya, lokacin da Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata A gareshi yayi hijira daga Makkah zuwa Madina, Abu Ubaidah shi ma yayi hijira tare dashi. Lokacin da Annabi Muhammad ya’isa Madina, ya hada kowane baƙi ( Muhajir ) tare da ɗaya daga cikin mazaunan Madina ( Ansari ), tare da Muhammad bin Maslamah tare da Abu Ubaidah da ke sanya su ‘yan uwan juna cikin imani. Musulmi sun kasance cikin kwanciyar hankali a Madina kusan shekara daga kafin Qurayshu ta ɗibi dakaru don kai wa Madina hari.
Yaƙin a zamanin Annabi Muhammad SAW.
Yaƙin Badr
A shekara ta 624, yakin badar ya kaure tsakanin Musulmi da Kuraishawa, farko Musulmai sunyi yunkurin tare fataken kuraishawa a karkashin jagoranci Abu Sufiyan. Musulmi sun tare hanyan da ke tsakanin Madina da Makkah Abu Ubaidah ya shiga cikin babban yaƙin farko tsakanin musulmai da Qurayshawa na Makka, a yakin Badr. A wannan yaƙin, ya yi yaƙi da Mahaifinsa Abdullah bn al-Jarrah, wanda yake yaƙi tare da rundunar kuraishawa. Daga baya Abu Ubaidah ya kai masa hari kuma ya kashe shi.
An saukar da ayar Alqur’ani mai girma game da wannan halin da Abu ‘Ubaidah yayi:
Yaƙin Uhudu
A shekara ta 625, yakin Uhudu ya kaure tsakanin Musulmai da Kuraishawa. kuraishawa sun fito yakin ne sabo da daukan fansar wainda aka kashe da cikinsu na yakin Badar wanda Sarkin Makkah Abu Sufiyan ne ya jagoranci babban tawaga sannan Kuma Khalid bin Walid Ya jagoranci tawagan sojoji masu dawakai A yakin Uhud. A karo na biyu na yakin, lokacin da sojojin Khalid bin al-Walid suka fatattaki musulmai daga baya, suna canza nasarar Musulunci zuwa ga shan kashi, mafiya yawan sojojin musulmin sun fatattake su daga fagen daga, kuma mutane kalilan ne suka dage. Abu Ubaidah daya ne daga cikinsu kuma ya tsare Annabi Muhammad SAW daga farmakin sojojin Qurayshi. A wannan rana, Abu Ubaidah ya rasa biyu daga cikin hakoran gabansa yayin da yake kokarin cire wasu alamomin makamai biyu na Na Annabi Muhammad SAW wadanda suka shiga kumatunsa.