Tambayoyi a Musulunci

ANA CIKIN SALLAH SAI FARFADIYA TA BUGE LIMAN !


Tambaya
Assalamualaikum warahmatullah wabarakatuhu
Allah ya gafarta Malam tambaya ce:

Ana sallah a jam’i sai farfadiya ta buge Imam bayan raka’a 2, shin za su dora ne akai ko kuma sabuwar sallah za su fara?

Amsa
Wa alaikum assalam
Za su Dora ne daga inda Liman ya tsaya, tun da alwalarsa ce ta karye.

Kundayan fiqhu sun kawo FARFADIYA daga cikin abubuwa da suke jawo warwarewar alwala, idan alwalar Liman ta karye dasawa ake yi, ba sakowa ba.

Allah ne mafi Sani

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

28/02/2023

See also  IDAN IDI YA FADO A RANAR JUMA'A, ZA'A BAR SALLAR JUMA'A !!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button