RamadanTambayoyi a Musulunci

INA CIKIN SADUWA DA MIJINA A RAMADAN SAI ALFIJIR YA KETOTambaya:
Malam muna cikin saduwa da mijina a cikin wannan wata, sai muka ji kiran Sallar Assalatu, menene hukuncin Azumin mu?

Amsa:
To ƴar uwa, mutuƙar kuna jin kiran Sallar kun maza da sauri kun datse saduwar da kuke yi, to Azumin ku yana nan, amma in har kuka ci gaba da yi koda na second ɗaya ne, to Azumin ku ya karye, kuma za kuyi kaffara ku duka, idan kin yi masa biyayya, in kuma takura miki yayi, to zai yi kaffara ne shi kaɗai.
Duba Almugni: 3/65
_Allah ne mafi sani._
18/06/2015

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

See also  AL'ADATA TA RIKICE, SABODA SHAN MAGANIN TSARA IYALI

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button