TARIHIN SAYYADINA UMAR ƊAN KHAƊƊABI RALIYALLAHU ANHU (KASHI NA BIYU)
Yadda Musulunci Ya Ratsa Zuciyarsa
Umar ya musulunta a shekara ta biyar kafin hijira bayan talakawan Musulmi sun sha wuya sosai a hannunsa. To, ya aka yi ya musulunta? Wane irin sirri ne ya karya zuciyarsa a daidai wannan lokaci?
Tun da farko dai Allah ya yi masa gamon katar ne da addu’ar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Domin kuwa lokacin da ƙunci da wahala suka tsananta a kan talakawan Musulmi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya roƙi Allah ya ƙarfafi addininsa da ɗayan mutane biyu, duk wanda ya fi soyuwa zuwa ga Allah a cikinsu; Umar ɗan Khattabi ko kawunsa Abu Jahli ɗan Hisham. Zaɓin Allah sai ya faɗa a kan Umar.
Farkon bayyanar tasirin wannan addu’a shi ne lokacin da wasu raunanan Musulmi za su yi hijira zuwa Habasha sai Umar ya gamu da su. Sai ya tambayi Ummu Abdullahi ɗiyar Hantamah ina suka nufa? ta ce masa, za mu bar mu ku garinku tun da kun ƙuntata mana, kun hana mu ‘yancin mu yi addinin da muka zaɓa, kun hana mu saƙat kamar mu ba ‘yan gari ba ne. Za muje in da za mu samu sauƙi da kwanciyar hankali tun da ƙasar Allah faɗi gare ta. Da ta gama faɗin wannan magana sai Umar ya ce, Allah ya kai ku lafiya!
Wannan addu’a ta Umar kuwa ta bai wa kowa mamaki, domin ba a san shi da tausaya wa Musulmi ko kaɗan ba. Da Ummu ta faɗa ma Amiru ɗan Rabi’ah abin da ya faru sai ya ce ma ta, hala kina zaton Umar ya musulunta? Sai ta ce, eh, don na ga ya tausaya mana sosai saɓanin al’adarsa. Amiru ya ce, to sai in jakin gidansu ya musulunta!
Ana cikin haka ne wata rana Umar ya shiga Masallacin ka’aba domin ya yi ɗawafi ya gaida iyayen gijinsa, sai ya yi kiciɓis da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yana Sallah. A wannan karon sai ya ɗan mayar da hankali domin ya ji abin da Manzo yake karantawa. Aka yi daidai kuwa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yana karanta suratul Haƙƙah, sai karatun ya kama shi sosai har ya ce, wallahi Ƙuraishawa sun yi gaskiya da suka ce mawaƙi ne. Amma wallahi waƙarsa tana da daɗi. Bai rufe bakinsa ba sai Manzon Allah ya kawo inda Allah ke cewa:
)فَلَا أُقْسِمُ بِمَا تُبْصِرُونَ (38) وَمَا لَا تُبْصِرُونَ (39) إِنَّهُ لَقَوْلُ رَسُولٍ كَرِيمٍ (40) وَمَا هُوَ بِقَوْلِ شَاعِرٍ قَلِيلًا مَا تُؤْمِنُونَ (41)
Ma’ana:
To, ba sai na yi rantsuwa da abin da kuke iya gani ba. Da abin da ba ku iya gani. Lalle ne, shi (Alƙur’ani) tabbas maganar wani manzo mai daraja ce (Jibrilu AS).
Da Umar ya ji haka sai ya ce, to in ko haka ne boka ne kenan. Sai ya ji ance:
)وَلَا بِقَوْلِ كَاهِنٍ قَلِيلًا مَا تَذَكَّرُونَ (42) تَنْزِيلٌ مِنْ رَبِّ الْعَالَمِينَ (43)(
Ma’ana:
Kuma shi ba maganar boka ba ne. Kaɗan ƙwarai za ku iya tunawa. Abin saukarwa ne daga Ubangijin halitta duka.
A nan sai ransa ya ɗarsa masa cewa, to ko ƙarya ce yake yi? Sai karatun ya ci gaba:
)وَلَوْ تَقَوَّلَ عَلَيْنَا بَعْضَ الْأَقَاوِيلِ (44) لَأَخَذْنَا مِنْهُ بِالْيَمِينِ (45) ثُمَّ لَقَطَعْنَا مِنْهُ الْوَتِينَ (46) فَمَا مِنْكُمْ مِنْ أَحَدٍ عَنْهُ حَاجِزِينَ (47) وَإِنَّهُ لَتَذْكِرَةٌ لِلْمُتَّقِينَ (48) وَإِنَّا لَنَعْلَمُ أَنَّ مِنْكُمْ مُكَذِّبِينَ (49) وَإِنَّهُ لَحَسْرَةٌ عَلَى الْكَافِرِينَ (50) وَإِنَّهُ لَحَقُّ الْيَقِينِ (51) فَسَبِّحْ بِاسْمِ رَبِّكَ الْعَظِيمِ (52)(
Ma’ana:
Kuma da (Manzon Allah) ya faɗi wata magana, ya jingina ta gare mu. Da mun kama shi da dama. Sa’an nan, lalle ne, da mun katse masa lakka. Kuma daga cikinku babu wasu masu iya kare (azabarmu) daga gare shi. Kuma lalle ne shi (Alƙur’ani) tunatarwa ce ga masu taƙawa. Kuma lalle ne mu, wallahi, muna sane da cewa daga cikinku akwai masu ƙaryatawa. Kuma lalle ne shi (Alƙur’ani) wallahi baƙin ciki ne ga kafirai. Kuma lalle shi gaskiya ce ta yaƙini. Saboda haka, ka tsarkake sunan Ubangijinka, Mai girma.
Kafin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya gama sallah jikin Umar ya yi sanyi sosai, zuciyarsa ta sauya duk yadda ba a zato, amma dai lokacin bai yi ba tukuna.
Bayan kwana uku da musuluntar baffan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, Hamza, sai Umar ya gamu da wani daga cikin talakawan Musulmi sai ya fara gaya masa magana mai kaushi kamar yadda ya saba, a lokacin Musulmi sun fara jin ƙarfin yin magana saboda musuluntar Hamza, sai wannan bawan Allah ya kada baki ya ce masa, to, kai Umar ka na wahalar da kanka a kan matsalar da ko cikin gidanku ba ka magance ta ba! Umar ya ce, wane ne ya karkace a cikin gidanmu? Sai ya ce, ƙanwarka da mijinta.
Jin haka ke da wuya sai Umar ya fusata ya tasar ma gidan Fatimah ɗiyar Khattabi. Da ya isa sai ya ji sautin karatun Alƙur’ani, amma kafin a buɗe masa ƙofa sai da aka ɓoye takardun da ake karatu don gudun sharrinsa. Kafin Fatimah ta gama yin maraba da yayan nata tuni har ya kai ma ta duka yana neman a ba shi abin da ake karantawa. Da suka lura al’amarin nasa babu tausai ko kaɗan a ciki sai ƙanwarsa ta ce masa, an ƙi a ba ka, kuma Musulunci ko kana so ko ba ka so sai an yi. Ka yi duk abin da kake iyawa!
Nan take sai jikin Umar ya yi sanyi, hankalinsa ya fara dawo masa, ya ji kunyar wannan raini da ya janyo ma kansa daga ƙanwarsa wadda ta ke ganin girmansa tana mutunta shi. A cikin lumana sai ya nemi ƙarin bayani. Allah Sarki! Kafin marece Umar ya bi sawun Musulmi.