Tambayoyi a Musulunci

MIJINA MAZINACI NE, ZAN IYA JUYA MASABAYA?

Tambaya:
Assalamu alaikum, Allah ya hadani da miji mazinaci, shin in na daina hada shinfida dashi dan gudun daukar wani ciwo innada laifi?.

Amsa:
Wa alaikum as salam, abin da ya fi shi ne ki yiwa magabatansa bayani, don su tsawatar masa ya daina, in Kuma kin tabbatar ya dau cutar aids kina da damar da za ki je wajan alkali don ya raba auren, tun da musulunci ya yi umarni da tunkude cuta gwargwadon iko, in har miji yana ciyar da matarsa to ya wajaba ta amsa kıransa, wannan yasa daukar matakin hana shi kanki zai iya jawo muku rigima, sanya alkali ko magabaci a hukuncin shi ne daidai.

Allah shi ne mafi Sani.

Dr. Jamilu Zarewa

See also  HARAMUN NE SIYAN KAYAN SATA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button