TechWhatsApp

YADDA ZAKA IYA SANIN LAST SEEN NA WANI A WHATSAPP KODA YA RUFE LAST SEEN NASHISanin last seen na wani ko wata ya dogara ne akan wanda yake da ha’k’kin kula da wasu al’amura na mutun. Misali ‘kannanka ko ‘ya’yanka mata ko maza wanda bakaso suna cinye lokacinsu na karatu a online ko rashin yin bacci a lokacin daya kamata.

Zaka iya sanin duk wani lokaci da suka hau online da kuma lokacin da suka sauka, koda baka yin chat dasu, kai koda ma sunyi block naka a whatsapp madamar dai kana da number ‘dinsu na whatsapp.

Akwai manhajoji da dama da suke yin irin wannan aikin, amma kuma mafi yawansu suna baka kyautar yin amfani dasu ne na kyauta a kwana ‘daya, daga baya sai ka biya ku’di zaka samu damar ci gaba da aiki dasu. Amma ana amfani da Multi Space apps domin 6atar masu da bayananka dan ka sake cigaba da amfani dasu duk bayan kwana ‘daya ‘daya.

LAST LOG da WAREP
suna ‘daya daga cikin manhajoji da suke da sau’kin amfani wajen sanin log-time na wani ko wasu.

Last Log
Kai tsaye da kayi install nashi zai baka damar ka shiga “free trial” wanda zakayi aiki dasu a kyauta na tsawon 24hrs, sai ka saka lambar da kake son sani lokacin da ake hawa da sauka daga whatsapp da ita.

Warep
Shi kuma wannan manhajar yana neman ka saka email address naka kafin ka fara aiki dashi, sannan yana da features da suke bu’katar a saka password.

Warep yana da sauki sosai wajen yi maka lissafin adadin lokacin da target number ‘dinka yake 6atawa a online, sannan zaka iya sauke duka bayanan lissafin a DOC ko kuma ka tura ma wani.

Dalilin yin wa’dannan manhajoji baya wuce kula da muhimmancin lokaci, yawan hawa online ba tare da wata amfanuwa da mutun yake ba, kamar ilmantuwa ko kasuwanci, yana cinye mana lokaci matu’ka, kada ka yadda wani wanda kake da iko ko isa da kulawa da wasu al’amura na rayuwarshi ya wofintar da lokacinshi a online, kaima idan ka nayi ka dena domin asara ce babba a gare ka.

Allah yasa mu ribaci lokacinmu da ya rage mana, Amin.

See also  Matakan Da Zakabi Idan Kanason ƙirƙirar Shafin Yanar Gizo (Website)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button