Cikakken Tarihin hukumar Nbais
National Board for Arabic And Islamic Studies (NBAIS)
Tana daga Cikin Jarrabawowin Da’aka Amince dasu a Nigeria a Matsayin kammala Karatun Sikandire.
an kirkiri wannan hukuma a shekarar alif dubu daya da dari Tara da sittin karkashin jagoran cin Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto
domin taimakawa daluliban dake tsangayar ilimin Addini Muslunci
wanda a yanzu haka akwai makarantu fiye da dari tara da suke rubuta wannan jarabawar
Tabbas jarabawar tana da matukar muhimmanci domin idan ba mu sawo ta a jarabawa ta uku mafi daraja a wannan kasa ba za ta zama ta hudu
muddin dalibi bai zauna ya rubuta ta ba bai da satifiket din kammala karatun sa sabili da haka ne zaka ga dalibai yan aji ukun karshen sikandire masu karantar bangaren larabci suna kokarin dagewa da karatu domin su samu su tsallake wannan jarabawar
ana rubuta wannan jarabawa a cikin watan June/July
jarabawar ta kunshi darussa kamar haka
Quran
Fikh
adab
mandik
balaga
Tarikh
Nahawu
Alhukuma ( government)
Hadith
Dss.
dalibin tsangayar larabci yana da kyawu ya karanci wadannan kwasa kwasan a matakin degree, NCE,ND
sun hada da
Hadith Education
Arabic Education
Arabic/Islamic
Qur’an Science
Arabic grammar
Arabic Literature
Da sauransu.
Miftahu Ahmad Panda.