Tambayoyi a Musulunci

BABU BAMBANCI TSAKANIN WIWI DA GIYA A HARAMCI

Tambaya

Assalamu Alakum.
Malam ina da tambaya kamar haka: shin tabar wiwi tana daukan dukkanin hukunce- hukuncen da suka hau kan giya (barasa) ko kuwa akwai banbanci.Dafatan zanga amsan wannan tambaya

Amsa

Wa alaikum assalam,  mutukar ta amsa sunanta na WIWI kuma tana bugarwa, tabbas za ta dauki dukkan hukunce-hukuncen giya na haramci.
Annabi s.aw. yana cewa “Dukkan abin da yake sanya Maye giya NE,  kuma dukkan giya haramun ce” kamar yadda Nasa’i  ya rawaito a hadisi ingantacce,  wannan sai ya nuna haramcin shan WIWI da duk abin da yake sanya maye.

Allah ne mafi Sani.

Amsawa‚úć

*Dr. Jamilu Zarewa

See also  BA ZAI YIWU A KAFIRTA DUKKAN 'YAN SHI'A BA !

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button