RamadanTambayoyi a Musulunci

FITAR MAZIYYI GA MAI AZUMI


.
Na Farko dai Menene Maziyyi?
Iman Nawawi acikin Littafinsa mai suna
Al’majmu’u yana cewa maziyyi; Ruwa ne Fari mai fatsi-fatsi wato marar kauri yana fita ne yayin sha’awa karama, ba’a jin dadi lokacin fitarsa kuma baya tunkudar juna a lokacin fitar sa, mafi yawan lokuta ba’a sani lokacin fitar sa ba.
.
Maza sunayi mata suma suna fitar da
Maziyyi amma mata sunfi maza yawan fitar wa fiye da maza.
.
Hukuncin sa ga mai azumi Malamai sun samu sabani akan, shin Maziyyi yana karya azumi ko baya karyawa Amma magana mafi inganci baya karya azumi,
ya kasance maziyyi ya fita ne saboda kallon mace ko Kiss ko romance duka baya karya azumi.
.
Wannan shine Ra’ayi da mazhabar;
~Abu Hanifa R.A
~Iman Shafi’I R.A
~Imam Ahmad R.A acikin wata ruwayarsa, kuma
Ibn Taimiya ya rinjayar da wannan ra’ayi na Iman Ahmad.
.
Amma mu Malikawa wato Malikiyya Sun tafi akan Maziyyi yana karya azumi musamman ma in mutum ne ya jawo shi da Gangan to yakan karya mishi azumi kuma biya na kan shi.
.
Ibn Usaimeen yana cewa acikin Littafin sa na “Sharhul Mamta’un” Yana cewa Magana mafi inganci kuma wanda itace daidai shine maziyyi baya karya azumi, kuma wanda yayi maziyyi alokacin azumi azumin sa bai baci ba.
.
Ibn Baz yake cewa:
“Fitar maziyyi ga mai azumi baya karya
azumi wannan shine zance mai inganci awajan malamai magabata…….
.
Fatawa ibn Baz
Daga bayanan da suka gabata nanuna magana mafi inganci awajan Malamai magabata shine Maziyyi baya karya azumi, domin babu wani Nassi wanda nanuna cewar Maziyyi yana bata azumi.
.
Allah ne Mafi Sani.

See also  BAYANI AKAN AZUMIN SITTU SHAWWAL

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button