TechWhatsApp

YADDA AKE UNBANNED WHATSAPP NUMBER

A wasu lokuta da suka wuce baya, mutane da yawa sun samu matsala da whatsapp ‘dinsu wanda aka dinga yin banned nasu da whatsapp kasantuwar amfani da GB Whatsapp da sauran wasu manhajojin whatsapp ‘din da basu akan ‘ka’ida.

Gaba ‘daya na manta da ana yin banned na mutane a whatsapp yanzu sai da wani abokina yake tambayata yadda zaiyi ya bude whatsapp number wadda akayi banned. Hakan yasa naga ya kamata in ilmantar da wanda basu san yadda ake yiba, saboda idan hakan ya faru dasu ko ya faru da wasu na kusa dasu.

Shidai banned na number whatsapp yana farune ta dalilin yin amfani da wani manhaja na whatsapp wanda baya a saman ‘ka’ida, ko kuma wasu suyi report na whatsapp number ‘dinka, ko kuma yawan chanja wayar da whatsapp ‘dinka yake a sama a lokaci ‘daya.

To dai ga hanyar da zaka bi ka magance hakan.

Daga farko idan ka shiga inda suke gaya maka sunyi banned naka daga whatsapp sai ka wuce kai tsaye ka danna wajen da aka rubuta “support”

Zasu nuna maka wani waje da aka rubuta “describe your problem”

Anan zaka rubuta masu matsalarka, wadda kake bukatar su magance maka ita, a matsayinka na mai amfani da manhajarsu, kuma wanda suke cin riba dashi.

Sai ka rubuta kamar haka..

“My whatsapp number 07012345678 has been banned kindly unbanned it, thank you.”

Sai ka danna next, nan kuma zai kaika wajen FAX wanda zaka ga different questions, sai ka wuce kasa inda aka rubuta “these doesn’t match my questions”, sai ka danna wajen zasu kaika wajen da zaka za6i ta inda zaka tura masu sa’kon, anan ma sai ka zabi email, daga nan sa’kon da ka rubuta zai sauka wajensu, bayan sun bude zasu tura maka sa’ko ta email dinka.

See also  ZABABBUN WEBSITE 10 DOMIN DALIBAN ILIMI

Masha Allah, Allah ya taimaka, Amin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button