Tambayoyi a Musulunci

HUKUNCIN ASKE GEMU A MUSULUNCI



Tambaya :
Malam menene hukuncin tsayar da gemu shin wajibi ne ko mustahabbi?, sannan aske shi haramun ne ko makaruhi ne ?

Amsa :
To dan’uwa Annabi s.aw yana cewa : (Ku sabawa mushrikai, ku cika gemu, ku rage gashin baki), kamar yadda ya zo a hadisin Bukhari mai lamba ta : 5553 da kuma Muslim a lamba ta : 259.
Wannan yasa da yawa daga cikin malamai suka tafi akan wajabcin tsayar da gemu da kuma haramcin aske shi, har ma wasu malaman kamar Ibnu Hazm sun hakaito ijma’in malamai akan haka, kamar yadda ya zo a littafinsa na maratibul ijma’i shafi na : 157.
Malamai suna cewa har abin da aka rawaito daga wasu sahabbai kamar Ibnu Umar cewa suna rage gemu idan ya kai wani geji, to suna yi ne lokacin hajji saboda suna ganin hakan na daga cikin rage kazantar da alhaji yakan yi bayan ya gama aikin hajjinsa.
Sannan gemu na daga cikin abubuwan da ke karawa namiji kwarjini da kyau, shi ya sa za ka ga wanda yake aske shi yana kama da tsohuwar da kyanta ya disashe, kamar yadda Sa’adi ya fadi a Bahjatu kulubul abrar shafi na : 50
Saidai malamai suna cewa idan mutum yana garin da za’a iya kashe shi idan ya bar gemunsa, to zai iya askewa saboda lalura, saidai ya wajaba kowacce lalura kar ta wuce gwargwadonta .
Don neman karin bayani duba littafin : Wujubu I’ifa’ul liha .
Allah ne mafi sani .

Jamilu Zarewa
17\10\2014

See also  AN BIYA MIN AIKIN HAJJI SAI MJINA YA MUTU, SHIN ZAN IYA TAFIYA ?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button