Nasiha

Tausayin Annabi Ga Dabbobi



Idan muka ambaci addinin Musulunci sau da yawa kalmar farko da ke zuwa a rai ita ce zaman lafiya. Kalmar Islam ta samo asali ne daga kalmar ‘ sa-la-ma ‘ wadda kuma ita ce tushen kalmar

(Hakika, Mun zo musu da wani littafi (Alkur’ani) wanda Muka bayyana shi daki-daki da ilmi, da shiriya da rahama ga mutanen da suka yi imani.} (A’araf: 52).

Jinƙai Shi ne ainihin halin da ke tattare da tawali’u, taƙawa, kulawa, ƙauna, da gafara. A lokacin da ake ganin wadannan halaye a duniya, suna nuni ne kawai na rahamar Allah ga halittunsa.

Allah Ta’ala ya fadi a sarari cewa Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam) rahama ne ga dukkan talikai, ba wai ga iyalansa da abokansa ba, ga al’ummar Larabawa, ga mutanen zamaninsa, ko kuma ga dan Adam Kawai Ba.

{Kuma ba Mu aike ka ba, face domin rahama ga talikai.

Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kasance siffar rahama, ya tausaya wa duk wanda ke tare da shi, da iyalansa, da marayu, da abokai, da baki har ma da makiya. Yana kuma girmama muhalli da dabbobi cikin girmamawa da jin kai. Ya koya wa mabiyansa cewa saboda dabbobi daga cikin halittun Allah ne a kula da su da mutunci da kulawa.

Hadisan Annabi Muhammad (SAW) suna tunatar da mu cewa an sanya dan Adam a doron kasa domin ya zama majibincin halittun Allah. Yin mu’amala da dabbobi da kyautatawa da jinƙai ɗaya ne kawai daga cikin nauyin da ke cikin wannan riƙon.

Maganar Annabi Muhammad SAW da dabi’unsa sun bayyana a sarari da Tausayawa Halittu Ciki Har da Dabbobi.

Idan wani ya kashe tsuntsu don wasa, sai yayi kuka a ranar kiyama, Yace ‘Ya Ubangiji! Wannan mutumin ya kashe ni a banza! Bai kashe ni don wata manufa ba.’

Annabi (SAW) ya ce, “ Duk wanda ya kashe tsuntsu ko wani abu mai girma fiye da Shi ba tare da hakki ba, Allah zai yi masa hisabi ranar kiyama. ” Masu saurare suka ce, “Ya Manzon Allah, menene dalilin Yi masa Hisabi? Sai ya amsa ya ce, “ Ai, zai yanka shi ya ci, ba wai kawai ya sare kansa ya watsar ba. ( An – Nasai)

Musulunci yana fatan dan Adam ya rika mutunta dukkan dabbobi (dukkan halittu – tsuntsaye, halittun teku, da kwari) cikin girmamawa da daraja. Annabi Muhammad ya ci gaba da nasiha ga mutane da su nuna alheri. Ya haramta yanka wutsiyar Dabba.

Idan Annabi ya ga wata dabba wadda Aka Jibga Mata Kaya Mai nauyi, ko wadda ba ta da lafiya, sai ya yi magana da taushin Ga Ma’abucinta kuma ya ce , “ku ji tsoron Allah a cikin Tausaya Musu.” ( Abu Dawud)

Daya daga cikin Sahabban Annabi Muhammad yana cewa , “ Muna cikin tafiya a lokacin Annabi ba ya nan, sai muka ga wata tsuntsuwa da ‘ya’yanta guda biyu; Sai muka dauke su. Uwar tsuntsu tana zagayawamu tana dukan fikafikanta cikin bakin ciki Lokacin da Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya dawo sai ya ce, “ Wane ne ya wahalar da wannan tsuntsuwa da ya dauke Mata Ya’ya? Maido mata su. ( Abu Dawud ne ya inganta shi daga Albani).

A zamanin jahiliyya, camfin maguzawa da ayyukan shi*rka sun haɗa da azabtarwa da zaluntar dabbobi. Musulunci ya yi Allah wadai da hakan, ya kuma dakatar da duk irin wadannan ayyuka. A lokacin da Annabi Muhammadu SAW Da Sahabbansa suka yi hijira zuwa Madina, sai suka lura cewa mutane sun kasance suna Yanke kitsen wutsiyar tumaki domin abinci. Annabi ya hana su yin haka, ya ce: “Duk abin da aka yanke A jikin dabba tana raye, to, Mushe ne (wato haramun ne a ci). ( At-Tirmidhi)

Dole ne ‘yan adam su daidaita wajen mu’amalarsu da dabbobi. Dukkan halittu Allah ya sanya su a doron kasa domin mu amfana, Ba su kai Darajar da ɗan adam ba amma kuma bai kamata a wulaƙanta su ba.

Mai imani na gaskiya ga Allah yana nuna imaninsa ta hanyar girmama halittu baki daya, kuma dabi’un Annabi Muhammad SAW da ayyukansa wani misali ne mai haske na girmama duk abin da ya wanzu.

See also  Abin da ya kamata ku sani kan daren Laylatul Qadr

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button