Tarihi

Cikakken Tarihin Taliya (Spaghetti)

Tarihin Taliya (Spaghetti)

Daga Sufy mai Fuffuke Saliadeen Sicey

Wasu masana tarihi sun ce mai yiwuwa an fara ƙirƙirar taliya tun daga karni na 1 Kafin Haihuwar Annabi Isa AS, kuma asalin taliya ta fito ne daga Bangaren Italiyawa, mai yiwuwa ta fito ne daga abincin Larabawa da ake kira “itriyya” a lokacin a karni na 7 AD lokacin da Larabawa suka mamaye Yankin Sicily a Kasar Italy ????????. A karni na 12 Taliyar Siciliy ta taliya ta zama ruwan dare.

A wani Tarihin Kuma ya nuna cewa Marco Polo ne kawo taliya, Turai zuwa Italy lokacin da ya fara kawo ta daga China, Amma alamu sun nuna akwai taliya tun kafin tafiyarsa.

Yayin da masana ke ci gaba da bincike kan ko Sinawa ne ko Farisawa ne suka fara yin taliya, abin da muka sani shi ne a kasar Italy ne aka sa mata suna.

Spaghetti ta yadu a Italiya bayan kafa masana’antar spaghetti a karni na 19, wanda ya ba da damar samar da spaghetti mai Yawa don kasuwar Italiya.

Kalmar Spaghetti ????


Spaghetti kalma ce ta Italiyanci Wato spaghetto, ma’ana Liyafa
(musamman wanda ake yi wa taron jama’a)

Wanene ya kawo taliya Afirka?


Taliya Batazo Nahiyar Afirka Ba sai Bayan yakin duniya na biyu, a lokacin da aka kamo ‘Sojjojin Kasar Italy da yawa aka Ajiyesu a kasar Afirka ta Kudu a matsayin fursunonin yaki, kuma ta haka ne aka samu Tabbatuwar Al’adun italiyawa da Abincin su Ciki har da taliya a Kasar Afrika Ta Kudu.

Yaushe spaghetti ta zo Najeriya?


1972

Spaghetti irinta italiyawa yawanci ana yin ta daga durum Semolina da alkama. Kamfanin Flour Mills of Nigeria Plc ya kafa masana’antar taliya ta farko a Najeriya a shekarar 1972 kuma Ya kira ta da “Golden Penny Pasta”.

See also  Gwamna Zabiya Na Farko A Tarihin Najeriya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button