Jima'i

Hadarin Yin Wasa Da Matarka A Lokacin Al’ada



Karara Allah Ya Haramtamana kusantar matanmu a lokacin da suke cikin al’adarsu na ganin wata. Duba wannan ayar 2:222.

“Kuma suna tambayar ka game da haila Ka ce: Shi cũta ne. Sabõda haka ku nĩsanci mãta a cikin wurin haila kuma kada ku kusance su sai sun yi tsarki. To, idan sun yi wanka sai ku je musu daga inda Allah Ya umurce ku. Lalle ne Allah Yana son mãsu tũba kuma Yana son mãsu tsarkakẽwa.”


Duk yaren da mai karatu zai yi amfani dashi wajen fassara wannan ayar sai ya tabbatar da abubuwa guda biyu. Akwai nisantar mace wajen haila Ma’ana lokacin da take haila ba za ayi Jima’i da ita ba.

Akwai umurnin kada a kusanceta sai bayan tayi wanka tsarki. Nisanta ba irin na kyama ba na gudun motsa sha’awa.
Wannan ayar Kai tsaye Allah (SWT) Ya aikota zuwa ga Annabi Mohammad (SAW) domin baiwa masu tambaya akan abunda ya kamata namiji yayi da matarsa a lokacin da take al’ada.


Sai dai an samu wasu Hadisan da aka rawaito Ma’aikin Allah yana rungumar matansa a lokacin da suke ganin wankinsu. A gaba daya Hadisan nan babu inda aka rawaito cewa baya ga wannan rungumar da akwai wani abunda ke shiga tsakaninsa da su har sai bayan sun yi tsarki.

Sai dai ga masu bin Mazahabar Malikiya sun Kara da cewa namiji zai iya yin ko wani irin wasa da matar sa muddin dai ba zai sadu da ita ba. Fatawar data ci karo da Ayar Allah dama Hadisan da aka dogara da su.

See also  Yadda Zaki Rage Zubar Ni'imar Gabanki


Wannan fatawar da wasu ke amfani da ita ta sa ma’aurata da dama cikin halaka mai makon samun lada da albarkar dake cikin saduwa na ma’aurata sai suka dawo suna kwasan zunubi irin na mazina ta. Tunda zina sa saduwa da mace tana haila duk haramun ne.


A likitance, lokutan uku ne yafi kowani lokacin da suke jefe mata cikin tsananin bukatar namiji. Lokacin da tana gaf da suma al’ada, lokacin da take al’ada da kuma kwanaki 3 bayan ta kammala al’adarta. Wadannan lokutan suna matukar jefa mata cikin sha’awar Jima’i da ba duk mace bace zata iya hakura a tayar mata da sha’awa ba a biya mata shi ba.
A bangaren maza, ba duk namiji bane za a yi masa wasa a motsa masa sha’awa kuma yana da damar yin Jima’i da matarsa ya hakura.


Hakan yasa wasu Ma’auratan marasa hakuri suketa Jima’i da matansu a lokacin ganin watan su, a kokarin su na amfanin da fatawar wasa da juna a lokacin al’ada.
Babu inda aka rawaito Annabi yayi wasa da matansa suna al’ada. Haka kuma koda akwai Hadisin Annabi ba daidai yake da kai ba wajen iya danne sha’awar sa domin gudun sabawa Allah.


Shi Allah daYa haliccemu shi yasan raunin mu ta bangaren Jima’i, hakan Yasa Yace mu kauracewa matanmu idan suna al’ada har sai bayan sunyi tsarki. Don haka da zaran mutum yaki bin wannan umurnin yace zai yi akasin abunda Allah Ya umurta, zai iya tsintar kansa cikin sabawa Allah maimakon samun lada.


Shi dai al’adar ganin watan mata baya wuce kwanaki 10, don haka hakurin da mai mace guda zai yi bazai wuce na wadannan kwanakin ba. Idan kuma namiji ne mai mata fiye da guda yakan iya samun wata damar muddin ba an samu akasin dukkaninsu suna jinin a lokaci guda ba.

See also  Yadda Zaki Gamsar Da Mijinki


Shawara anan, muddin kasan kana da karfin sha’awa ko matarka na dashi. Amfani da wancan fatawar ba naku bane. Nisanta da kauracewan nan dai da Allah Yace muyi shine abun yi domin gudun zunubi ta hanyar halas.

Barkanmu da Y Ranar Jumma’a. Allah Ya Zama Jagoranmu A Dukkanin Abunda Muka Saka A Gaba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button