Tambayoyi a Musulunci

HUKUNCIN DAUKAR HOTO A MUSULUNCITambaya
Malam menene hukuncin daukar photo graph kamar na kyamara da waya da sauran su ?

Amsa
To ‘yar’uwa Annabi ﷺ yana cewa: “Wadanda suka fi kowa tsananin azaba ranar alkiyama su ne masu suranta mutane kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 5950, a wani hadisin kuma yana cewa: “Duk mai suranta mutane yana cikin wuta” kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 2110.
Saidai malaman wannan zamani sun yi sabani akan wacce irin sura ake nufi a cikin wannan hadisin, shin Photograph zai shiga ciki, ko kuwa?

1. Akwai wadanda suka tafi akan cewa kowacce irin sura da ake yi ta shiga ciki, don haka bai halatta a dau kowanne irin hoto ba, in ba na lalura ba kamar Passport ko hoton da ake bukata saboda tabbatar da wani abu.

2. Ya halatta a dauki photograph, saboda ya zo a wasu hadisan da suke haramta daukar sura cewa: “Su ne wadanda suke kwaikwayon halittar Allah” kamar yadda ya zo a Bukhari a lamba ta: 5610, Shi kuma photo grapp babu kwaikwayon halittar Allah a cikin shi, saboda inuwa ce kawai ake dauka, don haka sai ya halatta, tunda ba sura ce ta hakika ba, sai ya zama daidai yake da mudubi, kuma babu sabani wajan halaccin amfani da mudubi, saboda ganin sura

Zance mafi inganci shi ne rashin yawaita daukar hoto, saboda hotuna na daga cikin hanyoyin da suka jawo aka bautawa wasu, sannan kuma dalilan wadanda suka haramta Photograph suna da karfi, fita kuma daga sabanin malamai yana da kyau.

Don neman karin bayani duba Alminhajj na Nawawy 14\81 da kuma Fataawallajna Adda’ima mai lamba ta: 5807, da fataawa Ibnu-uthaimin lamba ta151.

Allah ne mafi sani.
10/11/2014

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

See also  HARAMUN NE SIYAN KAYAN SATA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button