Tarihi

Tarihin Rijiyar al-Ghars, Wadda Annabi Muhammad SAW Ya Yi Wasiyya Gare Ta



Rijiyar al-Ghars (بئر غرس) rijiyar ruwa ce mai tarihi a cikin birnin Madina, Saudi Arabiya.

A shari’ance an yi imani da cewa, Annabi Muhammad SAW Ya sha daga wannan rijiya sau ɗaya, sannan kuma ya nemi a yi masa wanka da ruwanta bayan wafatinsa.

Kalmar Gharas, ta na nufin “Noma da shuka.” Bilal Ibn Rabah ya kasance ya na kawo ruwan rijiyar ga Annabi Muhammad SAW.

Wannan rijiyar ruwa ta na kusan kilomita ɗaya da rabi a arewa da Masallacin Quba.

TARIHI

An haƙƙaƙe kan cewar, rijiyar ta samu ne a shekara ta (620 CE).

A cewar Fouad Al-Maghmasi, mai bincike kan tarihin Madina, ya ce, “Rijiyar al-Ghars ɗaya ce daga cikin ababe masu muhimmanci a Madina da aka danganta da Annabi Muhammad SAW.”

Rijiyar al-Ghars, ta na ɗaya daga cikin rijiyoyin da Annabi Muhammad ya fi so, kuma a kan kawo masa ruwan cikinta domin amfani.

Ibn Majar, ya karɓo daga Ali bn Abu Talib ya ce, Annabi ya ce: “Idan na koma Ga Mahalicci, ku wanke ni da fatun ruwa guda bakwai daga rijiyar al-Ghars.”

Richard Burton, shi ne mutum na farko da ya ambaci rijiyar a tarihin zamani. Burton wanda ya yi tafiya zuwa ƙasar Larabawa a cikin kusan farkon shekara ta Alif da Ɗari Takwas da Hamsin (1850s), ya rubuta a cikin littafinsa, mai suna “Personal Narrative of a Pilgrimage to Al Madinah and Makkah,” (Bir al-Ghars).

Gharas ko Ghurs, an ce, daga wurin da take kimanin rabin mil ne daga Masallacin Kuba, kuma wata babbar rijiya ce mai yawan ruwa da yalwa.

Ko da yake, yanzu rijiyar ta ƙafe, kuma an yi amfani da ita har tsakiyar wannan ƙarni na Goma Sha Tara kafin ƙafewar ta.

Rijiyar Gharas, wanda ke cikin kwarin Bat’haan a cikin yankin al-‘Awali, yanzu ta ƙafe kuma ba a amfani da ita.

Rijiyar na yanzu ta na kewaye ne a cikin bangon maɗauri kuma ba a bayar da izinin shiga ciki ba.

An gina bangon rufin tare da gungumen dutse da bulo da wasu turaku da aka tokare a sama domin killace ta.

A halin yanzu wurin ya na ƙarƙashin kulawar Hukumar Yawon Buɗe Ido da kayayyakin tarihi ta ƙasar Saudiyya.

MADOGARA:

موسوعة معالم المدينة : الآبار الأثرية النبوية بالمدينة المنورة[وصلة مكسورة] نسخة محفوظة 02 يناير 2017 على موقع واي باك مشين.

Burton, R. (1857). Personal narrative of a pilgrimage to Al-Madinah and Meccah. London: Longman.
Memories of the luminous city.
آثار ومعالم المدينة المنورة التاريخية

History of Madinah Munawwarah (Holy Mosques) – Muhammad Ilyas Abdul Gani.

Pictorial History of Madinah Munawwarah – Muhammad Ilyas Abdul Gani.

The pictorial Collection of the Most Peculiar Places in AlMadinah AlMunawwarah – Abdulaziz Kaki.
Saudi Commission for Tourism and National Heritage

See also  TARIHIN SAYYADINA UMAR IBN KHAƊƊABI RALIYALLAHU ANHU KASHI NA BIYAR

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button