Blogging

Menene Hosting, da kuma amfanin sa?

Menene “*Hosting*”?

Akan kira shi da “Hosting” ko kuma “Web Hosting” wato Hosting wata fasaha ce da ke bawa Computer da kuma mutane damar saka ko daura shafuka na rubutun ra’ayin kai a yanar gizo ko wanda akafi sani da “Blog” kokuma “Website” wanda haka ke bawa maziyarta damar samun abinda suke buqata ta hanyar amfani da wayoyin salula kokuma Computer tareda taimakon Data.
Wato Hosting shine filin shafin yanar gizo, wanda zaibaka damar ajiye Files dinka acikinsa kamar; *Audio*, Video, da sauransu..
A takaice dai acikin Hosting zaka ajiye Site dinka.

Bari kuji;

Wato shafukan yanar gizo (Blog/Website) suna zama ne a wasu na’ura na musamman wanda ake masu lakani da ‘Servers’ duk lokacin da mutum ke son ziyartar wani shafi a yanar gizo abinda mutum zaiyi shine; Rubuta address din Shafin a Browser dinshi, Misali; https://Saheel. Blogspot. com.
Sai mutum ya danna Enter daganan ita kuma wannan wayar naka kokuma Computer din naka zata shiga duniyar yanar gizo domin nemo wannan address da kasaka..

Wato yawancin Companies masu kula da wadannan na’urorin na “Hosting” wanda ake kira da “Web Host” sukan buqaci mutum ya samo address na musamman wanda akafi sani da “Domain” domin akwai buqatar hakan kafin a dora wani shafi a yanar gizo.
Idan har ya kasance kuma mutum bayada shi sukan iya taimaka wa ta hanyar jagorantar mutum yadda zai siya cikin sauqi..

Hosting ya kasu kashi da dama; amma wasu daga cikinsa akwai;

1. Karamin Hosting: (Small Hosting Services)

wannan ne na farko daga cikin jerin kashi na Hosting,
A wannan Hosting din akan baiwa mutum damar daura shafinsa a yanar gizo amma a kayataccen farashi sannan kuma yanada iyaka.
A wannan Hosting mutum yakan iya dora shafinsa na kai (Personal Website) kokuma na kasuwanci (Business Website) wanda bashida nauyi sosai..
See also  Matakan Da Zakabi Idan Kanason ƙirƙirar Shafin Yanar Gizo (Website)

2. Babban Hosting; (Large Hosting Services)

wannan tsarin yakan baiwa Companies da dama damar daura shafinsu a yanar gizo, kuma ba lallai sai Companies kadai ke amfani da wannan tsarin ba, mutane ma masu babban shafuka sukan iya yin amfani da wannan tsarin saboda girmansa da kuma ingancinsa.

3. Free Hosting:

wani filin shafin yanar gizo ne, da ake badashi kyauta, amma sai dai bashida inganci sosai, domin idan aka jima ba’a shiga ba zaidaina aiki har sai kaje ka farfado dashi, sannan ako wane lokaci zai iya Error, ya lalace..

Allah yataimaka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button