Jamb

Bayani Gameda Two Sittings Tareda Yadda Ake Amfani Dashi

•Menene Two Sittings ?


Two Sittings a Bangaren Ilimin Najeriya Yana nufin yin Amfani da Jarrabawoyin Kammala Makarantar Sakandire Guda Biyu, da Akayisu a Lokuta Daban-Daban, a Wasu Lokutanma daga Hukumomi Daban-Daban, Wadanda Kasamu Nasara a Wani Fannin a Jarrabawa ta Farko, kuma ka ƙara Samun Nasara a Wasu Fannonin a Jarrabawarka ta Biyu, Wadanne idan Kahada Jarrabawoyi Biyun Zasu Samar maka da Abinda Makarantu Suke Bukata Domin baka Gurbin Karatu ko Kuma Halartar tantancewa.

•Menene Yake Sanyawa Ayi Amfani da Two Sittings ?Ana Amfani da Two Sittings ne idan Yakasance bakaci Dukkannin Darussan da Ake Bukata Domin Baka Gurbin Karatu a Jarrabawa Dayaba, Kuma Sai Yakasance kanada Ragowar Abubuwan da Ake Bukata a Daya Jarrabawar taka, Misali Wajibine Sai Kaci English da Mathematics a Jarrabawarka Kafin a Baka Admission a Jami’o’in Najeriya, to Idan Yakasance Jarrabawoyi Guda Biyu kayi, Misali Kayi NECO da WAEC, Kuma Kasamu English a Neco Amman Bakada Mathematics, kuma Kasamu Mathematics a WAEC dinka Amman Bakada English, to a Irin Wannan Yanayin Zaka Iya Hada Jarrabawoyin Guda Biyu kayi Amfani dasu domin Neman Gurbin Karatu.Karanta : Yadda Zaka Duba Sakamakon Jarrabawarka ta WAEC a Sakon Message

•Shin Dukkannin Manyan Makarantun Najeriya Suna Karbar Two Sittings ?Kwarai da Gaske, A yanzu mafi yawa, koma ince Dukkannin Manyan Makarantu da Jami’o’in Najeriya Suna Karbar Two Sittings Domin Bada Gurbin Karatu, Saidai Amman Akan Samu Banbanci Akan Irin Jarrabawoyin da Makarantun Sukan Amince su Karba a Matsayin Two Sittings din.

•Shin Wadanne Jarrabawoyi Makarantun Najeriya Suke Karba a Matsayin Two Sittings ?


Hakika Mafi Yawancin Makarantun Najeriya suna Karbar Jarrabawoyi Daban-Daban a Matsayin Two Sittings Misali : Dukkannin Manyan Makarantun Kasarnan suna Karbar Jarrabawar NECO da Wata NECO din da Aka hadasu a Matsayin Two Sitting, koda Kuwa Anyisu A Shekaru Daban-Daban ne, kuma Koda Sun Kasance Jarrabawoyin SSCE da GCE ne, Haka Zalika Makarantun na Najeriya suna Karbar Hadakar Jarrabawoyin NECO da WAEC a Matsayin Two Sittings, Sai dai kuma wasu Makarantun Basa Karbar Hadakar Jarrabawoyin NECO da NBAIS, Ko NECO da NABTEB, Ko WAEC da NBAIS ko WAEC da NABTEB a Matsayin Two Sittings, Amman Mafi Yawancinsu suna Karbar Jarrabawoyin NBAIS da NABTEB suma a Matsayin Two Sitting.
Shin Wannan Rubutun Ya Ƙayatar daku ?.

See also  Tambayoyi (20) da suke yawan fitowa Physics a jarabawar JAMB tare da amsa

Kusanar damu ta Comment Box domin Kara Mana Karfin Gwuiwa, Haka Zalika Kunada Damar Sanar damu Idan Akwai Wani Bangare da Kuke Bukatar Muyi Muku Rubutu Akansa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button