TARIHIN SAYYADINA UMAR IBN KHAƊƊABI RALIYALLAHU ANHU KASHI NA 3
Umar Ya Zama Sarkin Musulmi
Sayyadina Abubakar (RA) ya ayyana Musulmi Umar a matsayin wanda zai gaje shi bisa ga shawararsu kamar yadda ya gabata. Don haka da Sayyaina Abubakar (RA) ya cika nan take mutane su kayi masa mubaya’a kuma ya kama aiki.
Wani muhimmin abinda ya kamata a sani game da khalifancin Umar shi ne kwarjinin da yake da shi matuƙa a idon jama’a. Amma kuma duk da haka talakawa sun more a lokacin khalifancinsa, domin kuwa ya kasance yana kula da al’amurransu ta ko wane fanni. Bayan dai kulawarsa da tsayuwar addini, Umar yana kulawa da jin daɗin rayuwar jama’a da inganta lafiyarsu da gyaruwar tattalin arzikinsu da samun kwanciyar hankali da zaman lafiya a tsakaninsu.
Irin kwarjinin da Sayyadina Umar (RA) yake da shi a zukatan jama’a ya sanya wata mata ta yi ɓarin cikinta a lokacin da ta samu labarin an kai ƙararta ga Sarkin Musulmi Umar. Wannan ya sanya Umar ya tara jama’a ya nemi shawararsu a kan wannan abinda ya faru don sanin ko diyya ta wajaba a kansa. Ya kuma yi aiki da ra’ayin Sayyidina Ali (RA) na biyan diyyar jinjirin da aka rasa.
Ba za mu yi mamakin wannan mata ba idan muka san cewa, manyan Sahabbai irin su Zubairu ɗan Awwam da Sa’adu ɗan Abu Waƙƙas sukan tafi wajen Umar da nufin gaya masa wata magana ko gabatar da wata buƙata, amma su je su dawo ba su samu damar yin haka ba saboda kwarjininsa da ya cika masu fuska. Ibnu Abbas ma duk da irin kusancin da yake da shi ga Umar amma ya yi shekara ɗaya yana son ya tambaye shi game da wata aya bai samu damar haka ba saboda kwarjininsa.
Wani wanzami kuma ya saki iska saboda tsoro a lokacin da Sarkin Musulmi Umar ya yi tari shi kuma yana yi masa aski.
Umar kansa ya kan damu wani lokaci da yadda jama’a suke fargabansa, har ma ya kan ce, Ya Allah! Ka san na fi tsoronka fiye da yadda su ke tsorona.
A game da kulawarsa da talakawa kuwa, Umar ya shahara da ziyarar sa ido wadda yake yi a cikin dare yana sintiri a tsakanin hanyoyi da gidaje don sanin halin da ƙasarsa ta ke ciki. A cikin irin wannan ziyarar ne yake gano idan akwai ɓarayi ko wasu miyagu ko maɓarnata masu fakewa a cikin duhun dare su yi aikin assha, ko kuma baƙo wanda bai samu masauki ba.
Da yawa Sarkin Musulmi Umar ya yi aikin agaji ga wasu talakawan da su ke da buƙata wadda ya gano ta a dalilin wannan sintiri da yake yi. Misali, ya samu wani baƙo tare da matarsa tana naƙuda su kaɗai a cikin wata bukka, sai ya dawo gida ya nemi matarsa Ummu Kulsum ɗiyar Ali don ta je ta taimaka ma wannan baiwar Allah, a lokacin da shi kuma ya ɗauki kayan abinci ya hada wuta ya yi masu dafuwa wadda mai jego ta ke buƙata.
Wannan sintiri na Umar kuma ya haifar da sauyin wasu dokoki da tsare tsare a gwamnatinsa. Misali, a dalilin haka ne ya sanya doka game da masu zuwa jihadi kar su wuce wata huɗu ba a dawo da su gida ba, domin ya ji wata mata ta matsu tana koke game da daɗewar mijinta a fagen fama.
Ya kuma sabunta doka game da rabon arziki inda ya sanya ma duk jaririn da aka haifa a Musulunci albashi na kansa bayan a da sai wanda aka yaye shi ne ake ba albashi, amma a cikin dare sai ya lura da wani yaro yana yawan kuka, da ya nemi bayani sai ya gano uwarsa ta yaye shi kafin lokaci don tana son a rubuta masa albashi. A kan haka ya yi wannan sabuwar doka.
Haka kuma ya canza ma wani saurayi da ake ce ma Nasru ɗan Hajjaj wurin zama ya tayar da shi daga Madina ya koma Basrah saboda ya ji wasu mata a cikin dare suna taɗi game da kyawonsa, da ya bincika sai aka gaya masa har yana shiga a cikin gidaje, don haka Umar ya ji tsoron aukuwar fitina a gidajen bayin Allah waɗanda suka je wurin jihadi suka bar matansu a gida, sai ya ɗauke wannan mataki don magance ta.
Ban da wannan kuma Umar ya kan zauna bayan ko wace Sallah don sauraren buƙatun talakawa. Ya kan kuma shiga kasuwa don ya gane ma idonsa abin da ke gudana don ya hana yin cuta. Misali, akwai lokacin da ya tarar da wani baƙo yana sayar da man kaɗe a kan wani farashi da ba a saba da shi ba, sai ya umurce shi da ya sayar a kan farashin da aka sani, ko kuma ya fita daga wannan kasuwa. Kuma ya kan hana yin kasuwanci ga wanda bai san yadda ake yinsa ba.