ChatGPT

Yadda ChatGPT yake aiki

Kowa Yana Ta Magana Akan ChatGPT…!

Amma ka taba tambayar kanka ya ChatGPT yake aiki?

ChatGPT babban yare ne na computer da akewa laqabi da (Language Model), wata fasaha ce ta computer da ta san yadda zata iya amfani da kalmomi tayi magana. A zahirin gaskiya ChatGPT bashi da wata fahimta ko kadan akan yare, abinda ya sani kawai shine ya zaiyi amfani da kalmomi.

“Akwai banbanci tsakanin iya magana da kuma sanin yadda zaka jera kalmomi”

An horar da fasahar ChatGPT ne dan yayi wani aiki da ake kira (Next Token Prediction). Bari kuji yadda abin yake:

Misali sai nace: “Na tafi restaurant zanci…” tom a nan gurin a matsayin ChatGPT na wanda yadan yadda zai jera da tsara kalmomi, sai kawai ya karasa da cewa “Na tafi restaurant zanci… abinci”.

Toh haka ChatGPT yake aiki, an yi masa horo ne akan ya karasa jimloli, ko kuma yayi hasashen wace kalma ya kamata ya saka a gaban kalma. Wannan shine abinda ChatGPT yake yi, saboda haka ka daina tunanin idan ka tambayayi ChatGPT tsayawa yake yayi tunani, a’a dubawa yake yaga wane kalmomi ne yakamata su biyo tambayar da kayi.

Sai dai kuma akwai wani abin mamaki da ChatGPT yake yi, banda kasancewar ChatGPT babban abinda ake kira (Language Model), akwai abinda yake yi mai suna “RLFHF” ma’ana (Reinforcement Learning From Human Feedback).

Misali idan kana yawan amfani da ChatGPT zaka ga akwai lokutan da zai baka jimloli, sai ya tambayeka a ciki wanne ne yafi zama daidai. Sannan wanne a ciki bai yi dadin fada ba, yana neman ka fada masa wanne yafi zama cikakkiyar Jimla.

Yana amfani da wannan bayanin da zaka bashi wajen daidaita da kuma saita yadda ya kamata ya dinga yin magana, sannan kuma yanayin yawan amfaninka shima yana kara koyar dashi. Tom haka abin yake aiki.

Idan ka tsaya kayiwa “AI” ainahin fahimta, to zaka gane ba wani abune na ban mamaki ba. Sannan ana maganar cewa “AI” zai mamaye aiki da yawa da mutane sukeyi, a’a mutanen da suke aiki da “AI” ne zasuyi replacing na wadanda basa yin aiki da “AI” din.

Wallahu Ya’alamu…..!

Author: Muhammad Abdulrahman Sheka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button