Nasir I. Mahuta

DALILAN DA SUKA SANYA AKWAI BUKATAR A CIRE TALLAFIN MAN FETUR GABA DAYA A NIGERIA


Mai karatu idan baka manta ba jiya mun waiwayi tarihi ne mun ga yadda Shugabanni da mu ka yi a baya suka dinga kokarin ganin sun cire tallafin man fetur gaba daya, amma a karshe sai dai su samu damar rage wani adadi daga ciki. A yau kuma za mu yi bayani ne akan dalilan da ya sa akwai bukatar a cire tallafin mai din gaba daya. Daga cikin dalilan akwai:

1. Economic burden
2. Fiscal sustainability
3. Market distortions
4. Corruption and smuggling
5. Economic diversification

ECONOMIC BURDEN

Tallafin man fetur a Najeriya ya dora wa Gwamnati babban nauyi na da ke wawushe kaso mafi tsoka na kudin da kasar ke samu. Maimakon amfani da wannan kudin don gudanar da abubuwa masu mahimmanci kamar kiwon lafiya, ilimi, tsaro, wuta, ruwa da kayan more rayuwa, ana kashe kaso mai yawa akan tallafin farashin man fetur. Wannan yana nufin za a samu karancin kudi a wadannan wurare masu mahimmanci.

Idan biyan tallafin man fetur zai haifar da rashin kudi a bangaren ilimi, tsaro, lafiya, kayan more rayuwa kuwa, hakan na nufin: Ilimi zai yi tsada sosai kuma harkar ilimi za ta ci gaba da lalacewa. Idan Fetur ya yi sauki amma ilimi kuma ya yi tsada, idan fetur ya yi sauki lafiya ta yi tsada, idan fetur ya yi sauki wuta ta yi karanci kuma ta yi tsada, idan fetur ya yi sauki tsaro ya zama barazana to kamar an gudu ne ba’a tsira ba.

A bangaren ilimi ba ri ka ji illar da tallafin man fetur ya yi wa Nigeria. A iya 2019 binciken da Statista ta ya ya nuna akwai students da ke karatu 22.7 million a Nigeria. Hakan na nufin wadanda adadin duk suna fama da tsadar ilimi da kuma tabarbarewarsa. Tsadar ilimin kuma da tabarbarewarsa ya sanya yara da yawa ba sa zuwa makaranta. A binciken da UNESCO ta fitar akwai fiye da yara 20 million da ba sa zuwa makaranta a Nigeria.

Daga January 2022 zuwa June 2022 (wata shida kenan) Nigeria ta biya Subsidy N1.372 trillion. Yayin da a gaba daya shekerar 2021 kudn budget da aka warewa bangaren ilimi N742.5 billion ne kacal. Kada ka manta yin budget ba ya nuna an yi amfani da adadin kudin, yana nufin an kiyasata za a kashe adadin idan gwamnati ta samu yadda ta ke so. Hakan na nufin subsidy din da aka biya a wata 6 kacal ya kusan ninka budget na bangaren ilimi na shekara daya.

Bincike ya nuna akwai Universities guda 170 a Nigeria a 2021, 79 na su private Universities ne, 43 su ne na Gwamnatin Tarayya, 48 kuma na Gwamnatin Jihohi. Hakan na nufin Universities na kudi sun kusa ninka adadin yawan na Gwamnati tarayya da na jihohi. Hakan na nufin Universities na kudi su ne ke jagorantar adadin yawan Universities na Nigeria. Kudin da aka biya tallafin man fetur na wata 6 kadai zai iya gina University 171 ( 8 billion per university).

Tabarbarewar ilimi ya sa daliban Nigeria da yawa suna komawa karatu a kasashen waje. CBN da kanta ta ce a iya 2022 Yan Nigeria sun kashe $1.38 billion ( kusan 975 billion, $1=N750) wajen biyan kudin karatu a kasashen waje. Adadin kudin da ya wuce kudin budge din ilimi na gaba shekarar 2021. Duka wannan ya faru ne saboda ana karkatar da kudin da ya kamata ace an sanya su a bangaren ilimi zuwa biyan tallafin man fetur domin mai ya yi saukin saye.

Toh, fetur ya yi sauki, amma ilimi ya yi tsada har ta kai Yan Nigeria na biyan fiye da kudin budget din Ilimi na Kasar domin neman ingantaccen ilimi a kasashen waje. Abin da zai ba ka haushi, yawan masu amfani da fetur bai kai yawan adadin daliban Nigeria da yawan wadanda ba sa iya zuwa makaranta ba. Hakan na nufin Tallafin man fetur na taimakon tsirarun mutane ne, yayin da ya ke jefa mafi yawan mutane cikin tsada da tabarbarewar rayuwa.

A bangaren lafiya kuma bari ka ji illar da subsidy ya yi wa Yan Nigeria. A gaba daya shekerar 2021 kudin da aka yi budget din kashewa a bangaren lafiya N547 billion ne. Adadin da bai kai kudin tallafin man fetur na wata 6 na 2022 ba. A Nigeria bincike ya nuna akwai Asibitoci guda 40,017, guda 10,655 Asibitocin kudi ne. Binciken ya kuma nuna kowanne mutum 1000 a Nigeria gado daya su ke da shi a asibiti. Wannan ya nuna yadda harkar lafiya ta lalace a Nigeria.

Bugu da kari, Yan Nigeria na fama da tsadar biyan kudin lafiya bayan tabarbarewar ma. Binciken ya nuna Yan Nigeria na kashe fiye da USD1.6 billion (N664bn at 415/$) kowace shekara wajen neman lafiya a Kasar waje. Hakan na nufin, kudin da Yan Nigeria ke kashewa ya wuce adadin budget din lafiya na kasar a shekara gaba daya. Gwamnati na biyan tallafin man fetur don fetur ya yi arha, yayin da tallafin man fetur din na cinye kudin da ya kamata a inganta lafiya. Hakan ya sa Yan Nigeria ke biyan kudin lafiya da tsada sosai. Ta wannan bangaren ma, an gudu ne ba a tsira ba.

Duk da lacewar tsaro da muhimmancinsa, a budget na 2021 N772.60 billion aka ware masa. Iya tallafin man fetur na wata 6 kadai ya kusa ninka budge na tsaro na shekara daya. Irin wannan misalin yana nan a kowanne bangare na rayuwar Yan Nigeria.

A takaice dai, tallafin fetur ya wawushe kaso mai tsoka na kudin da Nigeria ke samu, ya kuma hana ruwa gudu a sauran bangorin rayuwar Yan Nigeria. Yan Nigeria suna sayen fetur da sauki amma suna ninka biyan kudin a wasu abubuwan da ya kamata ace sun saya da arha.

Mai karatu wannan dalili na daya kenan, idan ba ka manta ba akwai dalilai 5 da na lissafa. A rubutu na gaba zamu yi bayani akan dalili na biyu.

See also  KA GWADA WANNAN SANNAN KA BANI LABARI

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button