Tech

YADDA AKE CONNECTING ANDROID XENDER DA COMPUTER

Ka ta6a ha’da wayarka da computer ‘dinka ta sashen xender dan kayi transfer na wani abu?

Bama rashin iya connecting na xender ta Android ba zuwa computer ba, wasu ma da yawanmu basu san ana iya connecting ‘dinba, bare ma suyi.

kuma ba wani abu bane mai wahala, sai dai idan kawai mutun bai sani ba.

Dan’uwa ko baka da computer nasan zaka so kasan yadda ake yin wannan connecting ‘din tsakanin xender ta Android da kuma computer, domin sanin yadda ake yi ‘din yana da matu’kar amfani, sannan zai iya maka amfani.

Muje ciki kaji matakan da ake bi……

Da farko dai zaka bude xender ta wayarka android, sai kaje daga gefen hannun damanka a sama inda keda wasu layuka guda uku, idan ka shiga inda suke zaka ga inda aka rubuta “Connect PC” sai ka danna wajen, daga nan zaka ga wasu bayanai sun fito na yadda ake yin connecting ‘din.

Matakin gaba da zaka bi shine ka kunna Hotspot na wayarka, sannan itama computer din ka kunna Wi-Fi nata ka kamo hotspot na wayarka sai kayi connecting nasu harda password duka sai ka saka, tunda dama wayarka ce kasan komai nata.

Daga nan sai ka koma wajen 6angaren wayarka daga cikin xender ‘din inda ka shiga wajen “Connect PC” ‘din zaka ga sun rubuta maka wani web address daga kasa, sai ka bude browser ta computer ‘dinka kamar Firefox sai kaje 6angaren ‘search bar’ ina nufin wajen da ake yin rubutu a danna search, a wajenne zaka rubuta wannan web address ‘din wanda ka samu daga cikin xender ‘dinka, bayan ka rubuta sai ka danna “ok” ma’ana search kenan, kar kayi tunanin bazaiyi ba dan baka kunna data daga wayarka ba, a’a kawai wannan connecting ne zakayi wanda ya shafi transfer na wasu files a tsakanin wayarka da computer.

See also  Yadda Zaka Gano Wayar ka Ta Amfani Da IP-Address Dinta

Bayan ka gama wannan zaka ga web address ‘dinda kayi search ya kawo maka bayanan xender ‘dinda kakeso kayi connect da computer, sannan zai tambayeka ka amince suyi connect kamar yadda itama daga wayar a cikin xender zaka samun sa’kon neman amincewar ha’duwa a tsakanin device ‘din guda biyu wato wayarka da kuma computer. Da zaran ka danna kalmar amincewa shikenan zasu ha’du.

Daga cikin computer zaka samu damar da zaka iya ganin duk wani file da yake acikin wayarka sannan kana da damar da zaka saukeshi zuwa cikin computer ‘din koma ka gogeshi baki ‘daya.

Allah ya taimaka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button