TarihiTarihin Sayyidina Umar

TARIHIN SAYYADINA UMAR IBN KHAƊƊABI RALIYALLAHU ANHU KASHI NA SHIDA (6)Tsakanin Umar Da Gwamnoninsa

Ana iya cewa, dukkanin gwamnoni a zamanin khalifancin Umar sun yi tasiri da tsarin tafiyar da al’amurransa. Mafi yawansu sun kasance masu tsentseni da gudun duniya kamarsa. Amma kuma duk da haka, Umar sai ya lisafta abin da gwamnansa ya tara na arziki idan lokacin ƙarewar aikinsa ya zo. Kuma da yawa waɗanda ya karɓe rabin dukiyarsu ya mayar a taskar hukuma saboda wasu dalilai da suka shafi tara kuɗi ta wata hanya ba albashi ba, kamar kasuwanci ko kiyo da sauransu.

Sarkin Musulmi Umar ya umurci duk gwamnoninsa da su rinƙa zuwa aikin hajji tare da jama’arsu domin su samu halatar taron shekara shekara da yake yi da su inda yake yi ma su gargaɗi a game da talakawansu. Ya kan ce da su, “Ban ɗora ku a kan talakawa ba don kuci dukiyarsu ko mutuncinsu ko ku zubar da jininsu. Na tura ku ne don ku tsayar ma su da Sallah, ku sanar da su addini, kuyi masu rabo a kan adalci.” Ya kan sanar da talakawa cewa, suna da ikon kawo ƙara idan gwamnoninsu suka cuta masu.

A ɓangaren gwamnoninsa da sauran sarakuna kuma, Umar ba ya yarda a wulaƙanta su. Don haka, duk talakkan da ya kuskura ya ci mutuncin basarakensa ko ya yi masa raini wanda bai dace ba to, Umar ba ya sassauta masa.

Jihadi Da Faɗaɗar Daular Musulunci A Zamaninsa

Dukkanin ayyukan jihadi da Sarkin Musulmi Abubakar ya soma sun samu kammala a khalifancin Umar.

A zamaninsa, an kasa ayyukan jihadi zuwa ɓangare biyu: Gabas wadda ta haɗa da Iraƙi da garuruwan Farisa har cikin ƙuryarsu, da kuma Yamma wadda ta haɗa da Sham da Misra da Libiya.

A Gabas an ci garuruwa masu ɗinbin yawa da suka haɗa da; Kaskar, Sabat, Al Mada’in (Hedikwatar Farisa), Jalula, Tustar, Jundai Sabur, da Nahawand. Sannan sai Hamadhan, Rayy, Ƙumsi, Jurjan, Ɗabaristan, Azrabijan da Khurasan. Duk waɗannan yankuna ne da birane da suka kasance ƙarƙashin Farisa.

Sai kuma sashen Turkiyyah da Isɗakhr da Fasa da Dara Bijird da Kirman da Sijistan da Mukran da dukkan garuruwan kurdawa.
A ɓangaren yamma kuma, musulmi sun lashe dukkan biranen Sham waɗanda suka haɗa da Dimashƙa da Fihlu da Bisan da Ɗabriyyah da Himsu da Ƙinnisrina da Ƙaisariyyah da birnin Ƙudus. Duka waɗannan sun kasance a ƙarƙashin mulkin Rumawa, sai Allah ya wargaza ikonsu ya bai wa musulmi nasara a kansu zamanin khalifancin Umar ɗan Khaɗɗabi.

Daga nan kuma sai ƙasar Misra wadda ita ce yanki na biyu a cikin riƙon Rumawa. Ita ma an samu nasarar buɗa garuruwanta kamar su Bilbis da Ummu Danin da Iskandariyyah da duk garuruwan da ke tsakaninsu. Sannan musulmi suka wuce zuwa Barƙa da Ɗarabulus a ƙasar Libya, suka kuma samu cikakkiyar nasarar shigar da su a cikin daular musulunci.

Kafin ƙarshen khalifancinsa Umar ya gama da manya manyan dauloli biyu da su ke da ƙarfin yaƙi da tattalin arziki a duniya wato, Farisa da Ruma. Ya kuma shigar da karantarwar addinin Musulunci har abinda ya kai birnin Sin ta gabas, ya kuma game kusan dukkan yankuna na duniyar wancan lokaci.

Da haka ne Musulunci ya wayi gari shi ne addini mafi ƙarfi wanda kuma hukumarsa ita kaɗai ce mai faɗa aji a duniya. Don haka sai aka kau da ƙabilanci da faɗace faɗacen al’ada da aka saba. Mutane suka samu walwala da ‘yanci a ƙarƙashin mulkin Musulunci.

See also  TARIHIN SHUGABAN KASAR AMURKA ABRAHAM LINCOLN

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button