Tambayoyi a Musulunci

ALLAH YA TSINEWA MAI AURAN KASHE WUTA !!!Tambaya
Assalamu Alaikum Allah ya jikan malan don Allah tambaya ke gareni mace ce Allah ya kawo qaddarar rabuwa da mijinta kuma ba a saniba Ashe akwai yaron ciki sai daga baya aka sani kuma suna son junansu sosai .shin malan ya halatta ba tare da sanin mijin ba ita taje tayi auren kisan wuta ?

Amsa
Wa alaikum assalam, in har saki uku ya yi mata bai halatta ta yi auren kashe wuta ba, idan ta yi aure a wannan halin ta sabawa Allah ta bangarori guda biyu:

1. Ta yi aure a cikin Idda, hakan kuma sabo ne babba, saboda Allah madaukaki yana cewa a suratu Addalak aya ta: (4) “Kuma mata masu ciki idan an sake su to iddarsu shi ne su haife cikinsu”.

2. Yin aurenta zai kai zuwa ga cakuduwar nasaba, tun da in har saki uku ne mace ba ta halatta ga wani mijin sai ta yi wani auran kuma an take ta, saduwa da ita a wannan halin kuma shayar da shukar wani ne da ruwan wani, Annabi yana cewa a hadisin Tirmizi mai lamba ta: (1131) ” Wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira to kada ya shayar da ruwansa ga shukar wani”
Idan saki daya ya yi maki ko biyu yana iya miki kome, ba sai kin yo wani auran ba ko kuma kin haihu.
Allah ya la’anci namijin da ya yi auran kashe wuta da Kuma aka yi saboda shi, kamar yadda ya fito daga bakin da ba ya karya

Allah ne mafi sani

Amsawa‚úć????

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

18/07/2018

See also  ALAMOMIN BALAGAR NAMIJI

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button