Tarihi

Wafatin Nana Khadijah bint Khuwaylid 10 Ga Watan Ramadan (Kashi na farko)



Kashi Na farko.

A Rana mai Kamar Ta Yau 10 Ga Watan Ramadan Shekaru Uku Ko Hudu Kafin Hijira Allah Ya Karbi Rayuwar Matar Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW) Ta Farko Khadijah bint Khuwaylid A Makkah Hejaz Arabia (Saudi Arabia) Tana da Shekaru 63 Ko 64 A Duniya. An binne ta a makabartar al-Ma’lat da ke Dutsen al-Hajun.

Mahaifiyar Fatima (AS) Ta auri Annabi Muhammad (SAW) shekaru 15 kafin Bi’tha (Hijira)(595 CE) kuma ita ce mace ta farko da ta musulunta. Khadija (AS) ta sadaukar da dukiyarta wajen fadada addinin Musulunci. Annabi Muhammad (SAW) bai Auri wata mace ba a lokacin rayuwar aurensa da Khadija (AS). Manzon Allah (SAW) ya kasance yana yabon Khadija (AS) a rayuwarta da bayan rasuwarta.

Mahaifinta shi ne Khuwaylid ibn Asad ibn Abdul-Uzza ibn Qusayy kuma mahaifiyarta ita ce Fatima bint Za’ida. An ce haihuwarta shekara goma sha biyar kafin Am al-Fil /(555 CE)(Shekarar Giwaye) a Makka.

Bayanin Sanin Nana Khadija kafin Musulunci kadan ne. Kamar yadda majiyarmu ta bayyana, ta kasance hamshakiyar attajira ta dauki wasu mutane aiki domin su yi mata aiki.

Khadija tana da matsayi mai girma a cikin al’umma tare da Nasabar kakanni. Kamar yadda Ibn Sayyid Al-Nas ya ce: “Ta kasance mace mai daraja da hikima, kuma Allah ya yi mata albarka. Har ila yau, al-Baladhuri ya ce: “Al-Waqidi ya bayyana cewa Khadija tana da daraja ta kakanni, kuma ta kasance ‘yar kasuwa mai nasara”.

Khadija (AS) ita ce farkon matar Annabi Muhammad (SAW) kuma mace ta farko da ta musulunta.

See also  TARIHI DA KUMA ASALIN TASHE A KASAR HAUSA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button