A Ranar 17 Ga Watan Ramadan Shekaru Biyu Bayan Hijra Wanda Yayi Dai-dai Da 13 Ga Watan Maris Na Shekara 622 Miladiyya aka Gwabza Yakin Badar a tsakanin Rundunar Musulunci da ta kafi*rai A Yakin Badar.
Yakin Badar shi ne yaki na farko kuma mafi muhimmanci tsakanin musulmi da mush*rikan kuraishawa a farkon tarihin musulunci.Yakin Badar Ya zo a cikin Alkur’ani, tare jajircewarsu musamman Ali (AS) da Hamza Sayyid al-Shuhada’ Yakin ya haifar da Gagarumar nasara ga musulmi.
Badar wuri ne da Larabawa suke taruwa, kuma ana baje kolin kasuwa a cikin watan Zul-qa’da na tsawon kwanaki takwas.
A halin yanzu, yankin Badar ya koma wani birni mai tazarar kilomita 155 daga Madina mai tazarar kilomita 310 daga Makka.
Kamar yadda wata shahararriyar ruwaya ta ce, yakin Badar ya faru ne a ranar Juma’a 17 ga Ramadan, 2 / Maris 13, 624 kuma a wata ruwayar a ranar Litinin, 17 ko 19 ga watan Ramadan a wannan shekara.
Dalili
Kafin hijirar Annabi Muhammad (SAWW) Zuwa Madina mushrikai sun cutar da su, da azabtarwa, da kuma korarsu, aka fitar da su daga gidansu da garinsu, aka hana su aikin hajji. Allah bai baiwa musulmi damar su tashi tsaye wajen yakar mushrikan kuraishawa ba, a maimakon haka an umarce su da su yi hakuri kawai.
Bayan sun yi hijira zuwa Madina, a lokacin da suke tunatar da juna irin zaluncin da mushri*kai suka yi wa musulmi, sai Allah ya ba wa musulmi damar Yakarsu.
Yakin Badar
Samun nasarar da Manzon Allah (SAWW) ya yi bayan hijirarsa daga Makka zuwa Madina, da kuma irin karɓar da mutanen Madina suka yi masa ya sanya kafiran Makkan cikin halin damuwa da kuma kara gaba da shi. Don haka suka fara tunanin hanyar da za su bi wajen kawo ƙarshen wannan addini na Musulunci da kuma wanda ya kawo shi (Annabi). Don cimma wannan manufa, kafiran Makkan da ‘yan koransu suka fara kawo hare-hare ga yankunan da suke kusa da garin Madinan da kuma lalata kayayyakin gonakin musulmi da kuma ɗiban ‘ya’yan itatuwan bishiyoyin musulman.
Ganin irin wannan shiri na makirci da kafiran suke wa musulmin da kuma Musuluncin ya sa Manzon Allah (SAWW) ya ƙuduri aniyar kai hari wa wasu hanyoyin da kafiran suke samun kuɗaɗen shigan da suke amfani da su wajen ƙulla irin waɗannan makirce makirce. A ɓangare guda kuma kafi×ran Makka suna nan suna ta shirye-shiryen soji don kawo gagarumin hari wa musulmi da kuma murƙushe su. Kafi×ran dai sun iya tara rundunar soji da ta kai mutane 1000, da ta haɗa da raƙuma 700 da kuma dawaki 100, don aiwatar da wannan ƙuduri na su.
Koda wannan labari ya zo wa Manzon Allah (SAWW) sai shi ma ya shirya rundunarsa ta mutane 313 da nufin fuskantar ka+firan, inda suka fito daga garin Madinan don taryar kafi=ran a waje.
Koda sojojin musulmai suka iso wani guri da ake ce ma Badar, sai Manzon Allah (SAWW) ya umurce su da su dakata a gurin su jira isowar sojojin kafi&ran. Koda kafiran suka iso wajen sai Manzon Allah (SAWW) ya tura Ammar bn Yasir da Abdullah bn Mas’ud don su je su leƙo asirin kafiran da kuma irin ƙarfin da suke da shi don a san yadda za a ɓullo musu. Inda waɗannan sahabbai suka je kuma suka dawo da labarin da suka samo.
Kafin a fara wannan yaƙi dai Manzon Allah (SAWW) ya miƙa tutan rundunarsa ne ga Amirul Muminina Aliyu bn Abi Talib (AS).
Wannan yaƙi dai na Badar an fara shi ne a ranar 17 ga watan Ramalana shekara ta biyu bayan hijira. A wancan lokacin dai, larabawa suna da wani tsari na yaƙi da suke bi, shi ne kuwa kafin a fara yaƙin wasu dakaru sukan fito su gwabza tsakaninsu. Don haka a yaƙin Badar ɗin ma hakan ne ta faru.
Koda ɓangarorin biyu (wato bangaren gaskiya da shiriya karkashin jagorancin Manzon Allah (SAWW) da kuma bangaren ƙarya da ɓata ƙarƙashin jagorancin Abu Sufyan) suka fuskanci juna, sai wasu kafir×ai guda uku, wato Walid, Shaybah da kuma Utbah suka fito don tinƙarar musulmin.
A nan wasu sahabbai Ansarawa guda uku suka fito, sai suka ki amincewa da su suka ce ai ba sa’oinsu ba ne. Sai Manzon Allah ya umurci Ali bn Abi Talib, Hamzah da kuma Ubaydah da su fito su tunƙare su. Inda ya ce wa Aliyu ya tunkari Walid, Hamzah kuwa ya tunkari Shaybah shi kuma Ubaydah ya tunkari Utbah. Koda aka fara gwabzawa, nan take Aliyu ya ka*she Walid, Hamzah ma ya sare Shaybah, shi kuwa Ubaydah Utbah ya ji masa ciwo, nan take Aliyu da Hamzah suka kawo masa ɗauki, suka ƙarasa Utbah.
Ta haka ne sojojin Musulmi suka fara samun nasara, tsoro da fargaba kuma ya shiga zukatan dakarun kafirci, inda wuri ya ruɗe, daga ƙarshe dai musulmi suka sami nasara, suka kashe da dama daga cikin kafir+ai da taimakon Aliyu bn Abi Talib wanda ya kashe mafi yawa daga cikin kafiran da aka ka*she a yaƙin. Kafi+rai suka watse suka gudu musulmi suka bi su suka ɗibi ganima da kuma fursunonin yaƙi suka dawo gida.
Wannan dai ita ce nasarar farko da musulmi suka samu a ɓangaren soji akan kafir*ai.
Yakin Badar ya kare ne da shahadar musulmi 14 (Muhajirun 6 da Ansar 8) da mutuwar mushrikai 70 tare da kame adadinsu. Ibn Qutayba ya ruwaito cewa an kashe sojoji 76 daga kafiran Kuraishawa, an kama 44. yayin da da yawa daga cikinsu suka gudu zuwa jeji suna jiran dare Yayi su tsere.
Duk da cewa yakin Badar bai wuce rabin yini ba, amma yana daya daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a farkon tarihin Musulunci. Manzon Allah (SAWW) ya ce, “Shaidan bai taba zama mafi rauni da gajiyawa ba kamar ranar Arafa ba, sai ranar Badar.
Annabi (SAWW) ya zauna a Badar na tsawon kwanaki uku. Sai ya aiki Zaid ibn Haritha dan Abd Allah ibn Rawaha zuwa Madina domin bushara da nasarar musulmi.
Yakin Badar ya dauki hankula sosai a tsakanin musulmi da Yahudawa da munafukai a Madina. Haritha da Abdullahi ibn Rawaha, ya ce ba mu san me suke magana ba. Da jin wannan labari sai manya-manyan Khazraj suka je Bi’ir al-Rawha suna taya Manzon Allah (SAWW) murnar nasarar da ya samu, kuma wadanda ba su halarci yakin ba suka nemi gafara.
Wani abin da ya biyo bayan yakin Badar shi ne damuwar Ansar da abokansu yahudawa. Don haka suka gargadi Yahudawa da cewa: “Ku rungumi Musulunci tun kafin abin da ya faru da Kuraishawa ya same ku.
YAKIN BADAR A CIKIN ALQUR’ANI
An ambaci yakin Badar a cikin Alkur’ani 3 , 12-13, 123-127, Qur’an 4 , 77-78 da, Qur’an 8, 1-19, 36-51, 67-71. Wadannan ayoyi suna kamanta yunkurin Mushr×ikai da bai yi nasara ba da na mutanen da suka gabata, musamman Fir’auna. Kur’ani ya ce dalilin wannan yakin shine Shaidan ya yaudare su .
Kamar yadda Alkur’ani ya ce, wasu musulmi sun ki shiga jihadi , alhali kuwa Allah yana taimakon muminai; ya Ya kunyata mush*rikai, Ya sanya su zama ‘yan kadan a idon musulmi, ya aiko da ruwan sama da sauran abubuwa domin ya albarkace su da nasara. Mafi mahimmanci, kuma a bayyane, mala’iku sun zo don taimakon musulmi kuma suka sanya su bajinta.