Tambayoyi a Musulunci

WA YA FI KOWA KARYA A CIKIN HALITTUN ALLAH ?



Tambaya :
Don Allah malam a cikin kungiyoyin gaba daya wadanda ake dangantawa da musulunci wadanne ne suka fi kirkiro abubuwan da ba su da alaka da musulunci, don su kare akidarsu ?

Amsa :
To dan’uwa gaba daya a cikin kunkiyoyin musulunci babu wadanda suka fi ‘yan shi’a karya, ga abin da daya daga cikin magabata yake cewa :
Ma’abota ilimi da masu hankali sun yi ittifaki cewa : Rafidha sune kungiyar da suka fi kowa karya, kuma karyarsu dadaddiya ce, wannan ya sa malaman hadisi suke banbance su daga mutane saboda yawan karyar su, ga maganganun wasu daga cikinsu :
Abuhatim Arrazy yana cewa : “An tambayi Malik game da rafidha (Yan shi’a) sai ya ce : “Kar ku yi Magana da su, kar kuma ku yi riwaya daga gare su, saboda suna karya”
Imamush Shafi’i yana cewa ” Ban taba ganin wadanda su ka fi iya shaidar zurr ba, kamar Rafidha”
Sharik kuma yana cewa : “Ina daukar ilimi daga duk wanda na hadu da shi amma ban da Rafidha, saboda suna yiwa Annabi s.a.w. karya”
Duk wanda ya jarraba su, sai gane tsananin karyarsu, ta yaya zuciya za ta amince da wanda karyarsa ta yi yawa ?.
Duba Minhaaj 2\467

Dr. Jamilu Zarewa

See also  ANA CIKIN SALLAH SAI FARFADIYA TA BUGE LIMAN !

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button