Tarihi

Tarihin Fidda (RA) Hadimar Nana Fatima (AS)Fidda Yar aikin gidan Fatima al-Zahra (AS). Manzon Allah (SAWW) ya sanya mata suna “Fidda”. An ambace ta a cikin hadisai dangane da haihuwar Imam al-Hasan (AS) da Imam al-Husayn (AS) da saukar ayar al-It’am, da kuma shahadar Fatima al-Zahra (AS). Ta iya karanta ayoyin Kur’ani kuma ta san ilmin Kwayoyin Halitta. Ana Tsammanin cewa ta kasance a wajen Waki’ar Karbala ita ma.


Fiḍḍa al-Nūbīyya (Da larabci: فضة النوبیة ) Asali


Fidda ‘yar asalin Nubiyya ce; wani birni a kudancin Sudan ko kudancin Masar a gabashin kogin Nilu. Wasu sun dauka cewa asalinta ‘yar kasar Indiya ce wasu kuma suna ganin cewa ‘yar sarkin Indiya ce.


A Gidan Fatima Zahra (AS)


Fidda ita ce yar aikin gidan Fatima al-Zahra (AS). Manzon Allah (SAW) ya aika da ita gidan Fatima (AS) ya ce mata Fidda (wato a zahiri tana nufin azurfa).

Fatima (AS) ta raba ayyukan gida tsakaninta da Fidda-wata rana ta kula da gidan, wata rana Fidda ta kula da shi.

Lokacin da Imam Hasan (AS) da Imam Husaini (AS) suka kamu da Rashin lafiya, Sayyadina Ali (AS) da Fatima (AS) suka yi alkawarin yin azumin kwanaki uku bayan sun warke, Fidda ta taya su, ta kuma yi irin wannan alkawarin. An saukar da aya ta 7 da ta 8 a cikin Alkur’ani ta 76 dangane da haka.


Shahadar Fatima al-Zahra (AS)


A lokacin da Imam Ali (AS) ya kira ‘ya’yansa don yin bankwana da mahaifiyarsu Fatima (AS) Bayan wafatin ta, ya yi magana da Fidda ita ma: “Ya Ummu Kulthum, Ya Zainab, Ya Sukayna, Ya Fidda, Ya Hasan, Ya Husayn. zo ka yi bankwana da mahaifiyarku.
See also  TARIHIN SAYYADINA UMAR IBN KHAƊƊABI RALIYALLAHU ANHU KASHI NA BIYAR


Miji Da Yara


Bayan shahadar Sayyida Fatima (AS) Fidda ta yiwa Imam Ali (AS) hidima. Ta rayu tsawon shekaru 20 bayan haka. An san ta da mace saliha kuma mai hakuri. Imam Ali (AS) ya aurar da ita ga Abu Tha’laba al-Habashi wanda Su ka Haifi Da’

Bayan rasuwar Abu Tha’laba ta auri Abu Malik al-Ghatfani.
Danta ya rasu bayan wannan auren. Fidda ta haifi ‘ya’ya daga wurin Abu Malik. Wata yarinya mai suna Shuhra bint Muska bint Fidda wacce ake ce ta nuna wasu ayyuka na ban mamaki, jikar Fidda ce.


Halaye


Fidda ta yi Karatun ne da ayoyin Alkur’ani tsawon shekaru 20; ta amsa tambayoyin mutane da ayoyin alqur’ani. Akwai hadisi mai tsawo da ta yi karin bayani a kan yanayin da Fatima al-Zahra (AS) ta kasance tun wafatin Manzon Allah (SAWW) har zuwa shahadarta. Imam Ali (AS) ya ce game da ita: “Ya Allah ka albarkace mu a cikin Fiddanmu”.

A cewar wasu, ta san ilmin Kwayoyin Halitta Ance ta koyi shi ne daga Fatima al-Zahra (AS). Kuma Annabi (SAW) ya koya mata wasu addu’o’i da zikirin magance matsaloli. Halifa na biyu ya yarda da iliminta na addini.


Mutuwa


Akwai wani kabari a Damascus wanda ake danganta shi da Fidda. Yana cikin makabartar Bab al-Saghir. Kabarinta yana kusa da makabartar da aka danganta ga Abd Allah ibn Jafar ibn Abi Talib a yammacin karshen makabartar. Akwai wata ‘yar karamar kubba a dakinta kuma an yi katangarta da bakaken duwatsu.


A cikin Wakokin Addini


A cikin wakoki na addini da na al’ada, ana kiran Fidda a matsayin ‘yar aikin gidan Fatima al-Zahra (AS) da kuma nuna wasu kiramat (ayyukan al’ajabi). An ce ta sami Wannan karamarne saboda kasancewarta da Fatima (AS).

See also  TARIHIN OMAR AL-MUKHTAR

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button