Tarihin Abdullahi Ibn Umar (RA)

Tarihin Abdullahi Ibn Umar (RA) Kashi Na Daya (1)

Abdullahi ibn Umar ibn al-Khaṭṭāb (Da Larabci: عبدالله بن عمر بن الخطاب ) ko Ibn Umar ( ابن عمر ) (An Haifeshi Shekaru 3 bayan Bi’th yayi Wafati 73 / 692-3) yana cikin sahabban Manzon Allah (SAW) kuma dan Halifa Na Biyu Sayyadina Umar Ibn Khattab (RA) Yana dan shekara goma ya musulunta tare da mahaifinsa kuma ya yi hijira zuwa madina kafin mahaifinsa.

Ruwayoyin Ahlus-Sunnah sun Ambaci Cewa Mutum Ne mai saukin kai, Ya yi mubaya’a ga halifofi uku na farko bayan Wafatin Annabi (SAW). A lokacin mulkin Imam Ali (AS) duk da cewa ya ambaci falalolin Imam (AS) da dama Amma bai yi masa mubaya’a ba; amma daga baya ya yi mubaya’a ga Yazid Ibn Mu’awiya. Lokacin da Imam al-Husain (RA) zai Tafi zuwa Kufa, Abdullahi ibn Umar Allah ya bashi Shawarar Kada ya tafi yaki da Yazid.

Ibn Umar ya rasu yana da shekaru 84 kuma an binne shi a makabartar Muhajirai a Fakhkh.

Abdullahi ibn Umar ibn al-Khattab (RA) ko Ibn Umar yana cikin sahabban Manzon Allah (SAWW), dan halifa na biyu kuma surukin Manzon Allah (SAWW). An haife shi shekaru uku bayan fara kiran Manzo (SAWW). Mahaifiyarsa ita ce Zainab ‘yar Maz’un. An ce ya musulunta tare da mahaifinsa kuma ya yi hijira zuwa Madina kafin mahaifinsa. Sai dai wasu Ruwayoyi sun yi sabani game da shekarar da ya karbi Musulunci.

Ibn Umar ya kasance mai taka tsantsan a rayuwa don haka ya kasance mai taka tsantsan a cikin Yanke Shawara. Ruwayoyin Ahlus-Sunnah sun yi bayaninsa a matsayin mutum mai nisantar jayayya da mutane Ya ce: “Ban yi yãƙi a lõkacin fitina ba, kuma ina bin wanda ya yi nasara a sallar jam’i” su ka ce a cikin Hukunci Abu Musa al-Ash’ari ya ba da shawarar a Baiwa Abdullahi ibn Umar Halifanci, amma Amrul-As ya ce A’a bai cancanta ya yi mulki ba.

Abdullahi ibn Umar A Zamanin Manzon Allah (SAWW)

A yakin Badar da Uhud, Abdullahi ibn Umar yana yaro, don haka Annabi (SAW) bai bar shi ya shiga wadannan yakukuwan ba. Yakin Khandaq shine yakin farko lokacin da aka bashi izinin shiga. Ya kasance Yana da shekaru 15 a Lokacin wannan yakin. Ya shiga yaƙe-yaƙe kamar haka:Majiyoyin tarihi na Ahlus-Sunnah sun ruwaito cewa a yakin Muta lokacin da shi da wasu musulmi suka ji cewa makiya sun kusa samun nasara a yakin, suka tsere daga fagen fama suka koma Madina. Bayan sun tsere ne suka nemi gafarar Manzon Allah (SAWW) kuma aka gafarta musu.

Lokacin Halifofi Uku Na Farko

Ba a ganin Abdullahi bn Umar yana da tasiri a siyasa da mulki. Akwai ‘yan rahotanni game da shiga yaƙe-yaƙe. Bayan wafatin Annabi (SAW) a zamanin halifancin Sayyadina Abubakar (RA) Abdullahi ibn Umar yana cikin rundunar Usama.

A lokacin halifancinsa Sayyadina Umar (RA) ya kafa majalisa ya Nada Abdullahi ibn Umar a matsayin mai ba shi shawara, amma bai bar shi ya gabatar da kansa a matsayin dan takarar halifanci bayan Wafatinsa ba. A wannan lokacin, ya shiga yaƙe-yaƙe na Nahavand da yaƙin Masar.

Majiyoyin tarihi sun ambaci cewa bai taɓa yin hukunci ba. A lokacin da Sayyadina Usman (RA) ya ba shi wannan matsayin, Abdullahi ibn Umar ya yi magana a kan bai yarda da Matsayin da aka bashi ba. Yazid ibn Haruna ya ruwaito cewa, Ibn Umar ya gaya wa mutane cewa, “Na kasance tare da wanda ya fi ni hikima, kuma da na san kuna son hukunci a wurina kuma kuna tambaya, dana koya.”

Bayan kashe Sayyadina Uthman (RA ) wasu mutane ciki har da Marwan ibn al-Hakam Sun so a Ba shi halifanci; Abdullahi ya ce, ” ba zai karba ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button