Tarihi

KISSAR ABDULLAHI BN MAS’UD ابوعبدالرحمان عبدالله بن مسعود بن غافل بن حبیب الهُذَلی DA ZADANIL KINDYAn rawaito daga Abdullahi Bn Mas’ud, (RA) wata rana ya wuce ta wani wuri a garin Kufa (Iraƙi) sai ya tarar da matasa Fasikai sun taru suna shan giya kuma a cikin su akwai wani Mawaki ana kiran: Zadani yana buga ganga yana waka ga shi yana da sauti mai dadi.

Lokacin da Abdullahi Bn Mas’ud, (RA) ya ji muryan shi sai ya ce: ya kai mai kyaun wannan sauti ina ma da a ce littafin Allah ake karantawa da shi. Bayan ya fadi wannan magana sai ya ja mayafinsa ya rufe kansa ya wuce.

Lokacin da Zadani ya ji abun da Abdullahi Bn Mas’ud (RA) ya fada sai ya ce: wane ne wannan? Aka ce masa Abdullahi Bn Mas’ud ne (RA) Sahabin Manzon Allah, Sallallahu Alaihi Wa Sallama, sai ya ce me ya ce?, sai suka ce cewa ya yi:

me ya kai mai kyaun wannan sauti ina ma da a ce littafin Allah ake karantawa da shi.

Jin haka ke da wuya Zadani ya mike ya dauki sandan da yake buga ganga da shi ya karya shi, ya yi sauri ya je ya samu Abdullahi Bn Mas’ud, (RA) yana dauke da ganga a wuyar shi ya tsaya a gaban Abdullahi Bn Mas’ud yana kuka. Ganin haka shi ma Abdullahi Bn Mas’ud (RA) ya rungume shi, shi ma yana kuka.
Sannan sai Abdullahi Bn Mas’ud ya ce: don mene ba zamu so wanda Allah Ta’ala yake son shi ba alhali ya tuba daga zunubin shi.

Daga wannan lokaci Zadani ya lizamci Abdullahi Bn Mas’ud, Radhiyallahu Anhu, har sai da ya koyi Al-Qur’ani a wurin shi, kuma ya samu ilimi mai yawa a wurin shi har sai da ya zama jagora a cikin ilimi kuma Rawaito hadisai daga Abdullahi Bn Mas’ud da Salman wasu daga cikin Sahabbai, Allah Ta’ala Ya kara yarda a gare su.

See also  Cikakken Tarihin Facebook


Madgorar Wannan Rubutu


A duba littafin Kitaabut Tawwaabeen na Ibn Qudaamah al-Maqdisee shafi na 143.

Kadan daga cikin Abin lura wannan Tarihi

1, Magana koda kadan ce tana tasiri matukar an fade ta don neman yardan Allah, don haka ku zamo mai kira zuwa ga Allah.

2. Kofar tuba a bude take babu kuma mutum zai iya gyara rayuwar shi ya inganta ta kuma Allah Ta’ala Ya karbe shi.

3. Janyo wanda ya bace a cikin sabon Allah jika tare da tausaya masa.

4. Duk wanda ya nemi ilimi da gaske Allah Ta’ala zai bashi.

5. Kyawawan Halayen da Dabi’u, Na Wani Babban Jigo Na Sanya Mutum Musulmi, Ya Zama Mumini!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button