Tambayoyi a Musulunci

IDAN YARO YA YI KISAN KUSKURE, ZAI YI AZUMI SITTIN (60) A JERE !Tambaya
Salamun alaikum
Allah Ya taimaki Malam.
Mace ce ta aika yaronta dan shekara (13) ya debo kuka, ya hau sama sai ya saro ice, bai rike shi ba, ya fado ya kashe yarinya ‘yar shekara (4), Yanzu malam, dangin yarinyar sun yafe, wane ne zai Yi Azumi, Uwar ce za ta Yi, tun da yaron bai balaga ba ?

Amsa
Wa alaikum assalam
Yana daga cikin Ka’idojin Sharia
إذا اجتمع المتسبب والمباشر فالضمان على المباشر
Idan wani ya zama sababin samun asara ko kisa, wani kuma asarar ta faru a hannunsa, to Wanda ta faru a hannunsa shi zai biya.

A Mazhabobi guda uku ciki har da Malikiyya, idan yaro ya yi kisan kuskure zai Yi kaffara, kamar yadda ya zo a Muktasarul Khalil da Almugni na Ibnu Khudaama.

A bisa haka wannan yaron zai yi Azumi guda (60) a jere.

DUK hukuncin da Sharia ta alakanta shi da sabab to yana tabbata idan aka samu sabab din, kamar yadda yake a ilimin USULUL FIQH, wannan yasa balaga ba za ta yi tasiri a nan ba.
Da Mahaukaci da yaro da mai hankali su kan yi daidai a Hukunce hukuncen da Sharia ta alakanta samuwarsu da sababinsu ko sharadinsu kamar Zakka.

Allah Ne Mafi Sani.
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

20/11/2022

See also  ANNABI MUHAMMAD (SAW) BA YA KASHE WANDA YA ZAGE SHI !

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button