Tarihin Muhammad ibn Abi Bakar ibn Abī Quḥāfa

Tarihin Muhammad ibn Abi Bakar ibn Abī Quḥāfa (RA) Kashi Na (1)


Muhammad ibn Abi Bakar ibn Abī Quḥāfa (Da Larabci: محمد بن أبي بکر بن أبي قحافه ) ( Dhul-Qa’da 10 /February 632– Safar 38 /Yuli 658) yana daga cikin makusantan Imam Ali (AS) wanda ya nada shi gwamnan Masar.

Shi ne auta ga khalifan Musulunci na farko Sayyadina Abubakar (RA) Mahaifiyarsa ita ce Asma bint Umais, amma bayan rasuwar Abubakar, mahaifiyarsa ta auri Imam Ali (AS) don haka Muhammad ya tashi a gidan Imam (AS). Imam yana sonsa kuma yana daukarsa a matsayin dansa. wani lokaci ana kwatanta shi da na Abu Dharr a cikin zuciyar Manzon Allah (SAWW).

A zamanin halifancin Imam Ali (AS) yana daya daga cikin shurtat al-Khamis kuma kwamandan wani bangare na sojojin Imam (AS) a yakin Jamal da Siffin. An yabe shi a madogarar tarihi da na hadisai. Ya yi shahada lokacin da sojojin Sham suka mamaye Masar.).

Haihuwa Da Asalinsa

An haifi Muhammad ibn Abi Bakr a Watan Zul Qa’da, 10/ February, 632 a wani wuri da ake kira Dhul-Hulayfa (kilomita 18 daga Madina akan hanyar zuwa Makka), a lokacin da Manzon Allah (SAWW) yake kan hanyarsa zuwa Makkah domin aikin Hajjinsa na karshe.

Mahaifinsa Abubakar (RA) shi ne halifa na farko bayan Annabi (SAW). Ya rasu a lokacin da Muhammadu yake da shekara biyu da watanni da yawa. Mahaifiyarsa, Asma’ bt. Umays, ta kasance daya daga cikin fitattun matan Musulunci na farko. An fara aurenta da Ja’afar ibn Abi Talib (RA) kuma bayan shahadar Ja’afar ta auri Abubakar (RA).

Girma a Gidan Imam Ali (AS).

Bayan wafatin Abubakar, Asma’u ta auri Imam Ali (AS) don haka Muhammad ya rayu kuma Imam (AS) ya Rike shi Muhammad ya kasance yana da masaniya kan salon rayuwar Imam (AS) da halayensa, wanda hakan ya sanya shi son Imam (AS) sosai. Haka nan Imam (AS) yana son Muhammad kuma yana kiransa da “Dana”. A cikin Nahj al-balagha, an ruwaito cewa Imam (AS) ya ce: “Shi Sahabinna ne, kuma na rene shi kamar yarona.”

Hali da Imani

Yawancin tushen tarihin Musulunci na farko sun yarda da gaskiyar Muhammadu, adalcinsa, da girmansa. Kamar yadda ya zo a hadisi cewa, “Duk da cewa shi [wato Muhammad] bai kasance a cikin Ahlul Baiti (AS) ba, amma shi mutum ne mai daraja kamar su; shi ne mafi alheri da tsarkin zuciya a cikin iyalansa.” An ruwaito Imam Ali (AS) yana cewa: ” Allah ya gafarta wa Muhammadu! Muhammadu ya kasance yana son alheri ga mutane. Zai yarda da suka kuma ya nemi mutane su sanar da shi duk wani mummunan hali da za su iya gani daga gare shi.

Wurin da yake da shi a cikin zuciyar Imam (AS) daidai yake da na Abu Dharr a cikin zuciyar Manzon Allah (SAWW). Yana daga cikin makusantan Imam Ali (AS).

Ya dauki Imam Ali (AS) a matsayin mutum na farko da ya yi imani da Annabi (SAWW) kuma ya tallafa masa a tsawon rayuwarsa. Yasan cewa yaki da Mu’awiya yaki ne domin Allah wanda ya daukaka addininsa.

A lokacin Khalifancin Usman

Kasancewar Muhammad ibn Abi Bakr a cikin harkokin siyasa da na soja ya faro ne a halifancin Usman. Duk da cewa wasu malaman tarihi na yammacin duniya suna kallonsa a matsayin daya daga cikin wadanda suka shirya kisan Umar (RA) amma da alama wannan ra’ayi ba Gaskiya ba ne, musamman idan aka yi la’akari da cewa shekarunsa goma sha uku ne kacal a lokacin, ban da cewa babu maganar hakan a madogaran tarihin Musulunci na farko.

A lokacin halifancin Imam Ali (AS)

Muhammad yana daya daga cikin shurtat al-khamis a zamanin khalifancin Imam Ali (AS).

A Yakin Jamal

Yayin da ake shirin fara yakin, Imam (AS) ya nada Muhammad a matsayin kwamandan runduna. A lokacin yakin, Muhammadu ya nuna bajinta sosai; ya kashe Thawr ibn ‘Adi, daya daga cikin kwamandojin sojojin yakin Jamal. Sa’ad da yaƙi ya ƙare, sai ya yi wa sojojin da aka ci nasara alheri. Da umarnin Imam, cikin girmamawa ya dauki ‘yar uwarsa A’isha (RA) a cikin tawagar mata arba’in na Basra zuwa Makka daga nan zuwa Madina.

A yakin Siffin

Duk da cewa Imam Ali (AS) ya nada Muhammad a matsayin gwamnan Masar kafin yakin Siffin, amma bayanai sun nuna cewa Muhammad ya halarci wannan yaki da Mu’awiya. A cikin wani hadisi daga Imam Sadik (AS) an ruwaito cewa a yakin Siffin mutane biyar daga kuraishawa sun raka Imam (AS), daya daga cikinsu shi ne Muhammad ibn Abi Bakar. A cewar wasu rahotanni, Imam (AS) ya nada Muhammad a matsayin kwamandan runduna ko na bangaren hagu na sojojinsa.

See also  Tarihin Muhammad ibn Abī Bakr b. Abī Quḥāfa Kashi Na (2) Kuma Na Karshe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button