TALLAFIN MAN FETUR (FUEL SUBSIDY ) 01.
Fuel subsidy tsari ne da Gwamnati ke amfani da shi domin ganin mutanen Nigeria sun sayi fetur a farashi mai sauki. Kasancewar farashin fetur kamar fetur din ne a cikin mota, gwargwadon yawan fetur gwargwadon nisan tafiyar da motar za ta yi. Haka Gwargwadon tashin farashin fetur, gwargwadon tashin kayan da ke da na saba da Fetur wajen amfani, samarwa da sarrafawa za su yi.
Tun farko dai Shugaba kasa Gen. Yakubu Gowon ne ya fara kawo tsarin Fuel subsidy a Nigeria a 1970s bayan Nigeria ta samu nasara maida Ikon sarrafawa da gudanarwar danyen manta karkashin gwamnatin tarayya domin a samu daidaito na raba arzikin da ake samu ta sanadiyyar mai din.
Kasancewar a shekarar ne dai aka kammala yakin Biafra, wanda kafin hakan hatta wasu kasashen sun yi amfani da wannan damar wajen shiga cikin al’amarin mai. Kuma yakin ya haddasa karancin mai musamman a Arewacin Nigeria sakamakon sarrafawa da gudanarwa mai din baya hannun gwamnatin tarayya.
A lokacin da Yakubu Gowon ya samu nasarar maida duk wata gudanarwa mai a Nigeria karkashin gwamnatin tarayya, shi ne ya sanya tsarin tallafin man fetur da niyar yan nigeria su samu damar sayen fetur a farashi mai sauki. Sayen fetur a farashi mai sauki zai saukake zirga-zirga da kuma saukake kudin da kamfanoni ke kashewa wajen sarrafa kaya, wanda hakan zai sanya kaya su yi sauki.
A lokacin ne dai Gwamnatin Yakubu Gowon ta kirkiri ko in ce ta maida NNOC (Nigerian National Oil Corporation) zuwa NNPC (Nigerian National Petroleum Corporation) a 1971, a matsayin hukumar da za ta kula da samarwa, sayarwa tare da kula da rarraba mai din zuwa ga mutanen nigeria duka a karkashin Gwamnatin tarayya.
Samar da NNPC ya bunkasa adadin mai da Nigeria ke samarwa sakamakon hukumar ta kara gano rijiyoyin mai a gurare da dama tare da bukatunsa adadin mai din da Nigeria ke samarwa. A lokacin Nigeria ta zama daya cikin kasashe dake sahun gama wajen samar da danyen mai a a duniya.
A wancen lokacin Nigeria na da matatar mai guda daya ne kawai wadda ta ke a garin Port Harcourt mai suna ‘Alesa-Eleme Refinery’. A lokacin matatar na da girman iya tace 35,000 barrels ne kowacce rana. 35,000 barrels kuwa daidai ya ke da kusan 5,565,000 liters. Amma sakamakon yakin Biafra ba lallai idan tana aiki yadda ya kamata ba ma. A lokacin adadin mutanen nigeria ya kai 50 million, hakan na nufin kila adadin fetur din da Nigeria ke iya samarwa ya yi kadan ya wadatar da bukatuwar Fetur din a Nigeria, a dalilin haka Nigeria ba ta da zabin da ya wuce gina karin matatun mai.
NNPC ta yi kokarin gina karin matatar mai a kaduna (Kaduna Refinery) tun daga lokacin amma ba’a samu damar kammalawa ba sai a 1980 zamanin mulkin shagari. A lokacin, Kaduna Refinery na da girman iya tace 60,000 barrels ne ko wacce rana, watau 9,540,000 liters.
Kafin a samar da Kaduna Refinery mun ce adadin mai din da Alesa-Eleme Refinery ke tacewa kila ya yi wa Yan Nigeria kadan. Kuma ga shi Nigeria na Samar da adadin danyen mai din da ya wuce bukatuwar al’ummah. Wannan dalili na daga cikin dalilin da ya sa Yakubu Gowon ya kawo tsarin tallafin man fetur. Saboda Nigeria na sawo karin adadin fetur din da ake bukata a kasar daga wasu kasashen, sai ta yi amfani da kudin da ta sayar da danyen manta (crude oil) ta biya tallafin man fetur don Yan Nigeria su sayi mai a kasa da yadda Nigeria din ke sayowa a kasashen waje. Ko kuma domin a samu farashi bai daya na Fetur tsakanin yankin arewa da yankin kudu.
Misalin yadda Danyen mai (crude oil) da kuma fetur ya ke da abin da ya kawo tallafin man fetur shi ne:
Ka kaddara kai Manomi ne da ke noma alkama (wheat) wadda kamfanoni ke amfani da ita domin yin spaghetti. Kana da yara a kalla 20 wadanda suka yi aure da su ke bukatar ciyar da yaransu da spaghetti kuma duka nauyin samar masu da spaghetti din nan a hannunka ya ke.
Tunda kana bukatar Spaghetti amma kuma kamfanonin ke sarrafawa kai kuma ba ka da kamfani. Ko kana da kamfani kafin a maida alkama ta zama spaghetti dole sai an bi matakan sarrafawa da yawa wadda matakan na cin wasu adadin kudade. A dalilin haka ne ka ke zuwa kasuwa ka sayar da kowanne buhun alkamarka misali N2k. Kuma a kowace shekara kana iya noma alkama buhu 200 wanda kudinsu ya kai 400k. Farashin spaghetti a lokacin N70 ne, kuma a kowacce shekara yaranka masu auren nan suna bukatar sayen spaghetti a kalla kwali 1000, wanda kudinsu ya kai N70k.
A matsayinka na Uba domin ka tausaya masu shi ne ka ke amfani da N70k a cikin N400k na kudin alkamar da ka sayar, ka ke sawo masu kwalin spaghetti 1000 da su ke bukata, kai kuma ka sayar masu a N35. Hakan na nufin ka sanya masu tallafin N35 akan kowane kwali. Toh, kamar haka tallafin man Fetur ke aiki.
Kasancewar a lokacin Nigeria kila ba ta iya tace fetur din da Yan kasa ke bukata, kuma koda tana iya tacewar tana kashe kudi da idan za ta sayar da kowanne litter za ta sayar akan farashi 30, maimakon haka sai ta yi amfani da kudin da ta samu na sayar da danyen mai wajen sanya tallafi akan kowacce litar fetur da Yan Nigeria ke bukata.
Wannan shi ne takaiccen tarihin yadda tallafin man Fetur (Subsidy) ya fara. A rubutu na gaba za mu dora da bayanin yadda Subsidy ya ke har zuwa yanzu 2023.