Soyayya

Wasu Alamun Da Zaki Iya Gano Namijin Da Bai Damu Da Aure Ba



Da akwai mazan da suke haura shekarun da ya kamata ace sunyi aure amma sai aga basu Yi ba.


Irin wadannan mazan dai ba wai basu da lafiya ko rashin wadata bane, kawai dai aure ne baya cikin tsarin rayuwarsu.
Duk da haka ana samun matan dake likewa irin wadannan mazan duk da tunanin ko zasu auresu.


Ga wasu alamun da muddin kika namiji yana dasu kawai ki fitar harkarsa ba zai yi aure ba.

1: Haura Shekarunsa- Duk namijin da kika ga ya haura munzalin lokacin daya dace yayi aure kuma yana da lafiya da daman yin yaki yi, yana cikin irin mazan da aure baya cikin tsarinsu.
Kada ma ki bata lokacinki a wajensa ba aurenki zaiyi ba.


2: Yiwa Mata Gadara- Akasarin irin wadannan matan a kullum basu cika ganin darajar mata ba. A kullum suna yiwa mace kallon rashin yarda da kuma matsala.


Irin wadannan mazan a duk lokacin da zasu yi mu’amala da mace sai su rika hadawa da gadara. Ko nuna isa, basu iya rarrashin mace ba.


3: Basu Da Lokacin Yin Soyayya- Da wuya ki gansu suna son mace sai dai idan zina zasu yi da ita. Idan mace tace tana sonsu nan take zasu nuna mata sai dai idan zina zasu yi da ita.


Don haka idan kin fahimci wanda kike son haka yake kina batawa kanki lokaci ne.


4: Suna Yiwa Aure Kallon Wahala Ne- Sunfi mai aure iya tsara yadda zai zauna da matarsa. Sunfi nunawa ma’aurata kuskurensu daga waje. Haka nan gani suke idan ba ka mallaki wasu miliyoyi ba aure ba naka bane.

See also  Yadda Zaka Tinkari Mace Ba Tare Da Ta Zulle Maka Ba


5: Basu Da Sha’awar Haihuwa- Sune zaki ga suna da kushe haihuwa da kuma yawan yara. Sune zakiji suna tsara miki rayuwar da zasu yi idan sun yi aure da mace guda da haihuwa daya.


Sunada kakale da tsarafetsafe. Duk lokacin da aka musu zancen aure zasu ce lokaci ne baiyi ba.

Irin wadannan maza bayaga matsalar kwakwaluwa, har ila yau maza ne da suke da matukar hadari a cikin al’uma. Domin sune ake yawan samunsu da yiwa yara kanana a unguwa kwakule, Fyade, luwadi da yara da kuma lalata yara mata sabbin balaga.


Da fatan mutane zasu zurawa irin wadannan mazan idanuwa a unguwowinsu domin kada su batawa yaransu tarbiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button