Nasir I. Mahuta

IYA TURANCI BA YA NUNA KAIFIN BASIRA.

Hausa


Duk da na dan iya Turanci, amma ba na ganin iya Turanci a matsayin ma’auni da ke nuna mutum yana da tsanani basira. A wajena Turanci yare ne kamar kowanne yare misali, Hausa. A matsayina na Bahaushe ba na bukatar zuwa makaranta kafin na iya hausa. Komai rashin basirata zan tashi ina jin Hausa, irin Hausar da ko da wanda ba Bahaushe ba ya je makaranta ba lallai ya fi ni iya magana da Hausa sosai ba.

Duk da ya ke abin jinjinawa ne ga wanda ba Bature ba ya iya magana da yaren Turanci sosai, wanda hakan ya nuna ya koyi Turancin ne sosai. Iya koyar yaren da ba naka ba shi ma daya ne daga cikin nau’ikan basira guda 8 da mu ke da su:

1-Logical-mathematical intelligence
2-Spatial intelligence
3-Musical intelligence
4-Bodily-kinesthetic intelligence
5-Interpersonal intelligence,
6-Intra-personal intelligence
7-Naturalistic intelligence.
8-Linguistic intelligence

Iya Yaren da ba na ka ba kamar Turanci yana cikin nau’in intelligence da ake kira ‘Linguistic Intelligence’. Wadanda ke da Linguistic intelligence zai zama mai saurin koyon yaren da ba na shi ba. Duk da haka fa, yaren da su ke koyo din nan akwai wadanda sun iya yaren saboda native language na su ne. Hakan na nufin su ko da ba su da Linguistic Intelligence amma za su iya yaren da aka haife su cikinsa.

A gaba daya nau’ikan intelligence guda 8 da na lissafo, linguistic intelligence shi ne mafi rauni a cikinsu domin iya kokarin koyan yare kawai ya ke nunawa. Yayin da duniya na cike da ci gaban da sauran nau’ikan intelligences din su ka samar.

Amma yadda wadanda su ka iya Turanci ke kallon wadanda ba su iya ba a matsayin marasa basira ko fasaha abin na ba ni mamaki. Alhalin ko a Nigeria iya Turancinka na da nasaba da yadda ka taso; makarantar da ka yi da kuma abin da ka karanta a makaranta.

Idan tun daga tashinka an sanya ka makarantar da ake magana da turanci sosai, to duk rashin basirarka za ka iya magana da Turancin. Amma kafin ka iya, mathematics da sauran subjects din da ake koyarwa, dole sai kana da basira. Idan ka girma kuma iya Turancinka na da alaka da mai ka karanta a High level. Wanda ya karanci English dole zai iya fin wanda ya karanci Computer Engineering iya Turancin amma hakan ba ya nuna ya fi wanda ya karanci computer engineering din basira. Saboda, wanda aka haifa a matsayin Bature zai iya Turanci ko da bai je makaranta ba, amma ba zai iya computer engineering ba dole sai ya koya dole sai yana da basira . Shin ba ka lura ba ma a Nigeria wanda credentials na shi ba su cika ba shi ake tura bangaren koyon yare? ???? Rashin cikar credential na shi din nan yana nunawa Malamai cewa a kai shi bangaren da ake bukatar mafi raunin nau’in fasaha (Linguistic intelligence)

Wani lokacin iya Turanci ya danganta ne da inda ka ke zama.Misali a Nigeria, wanda ke zaune a yankin kudu zai fi wanda ke zaune a yankin Arewa sauri da saukin koyon Turanci. Saboda a Yankin kudu ana yawan magana da Turanci, hakan ya sa hatta wanda bai je makaranta ba yana iya magana da Turanci. A yankin arewa kuwa ba a cika magana da Turanci ba, shi ya sa zai fi wahala da ka iya turanci idan kana zaune a yankin arewa musamman arewa masu yammacin Nigeria.

Wani lokacin iya turanci yana da nasaba ne da addininka. Misali, Christian zai fi saukin koyon Turanci fiye da Musulmi sakamakon Bible din da Christian su ke karantawa mafi yawa English version ne. Haka Musulmi dole zai fi Christian sauri da saukin koyon Larabci saboda karatun addini da Musulmai ke yi suna yi ne cikin Larabci. Hakan ya samo asali ne saboda a tsarin koyo (socialization), makaranta ita ce ta lamba ta hudu a jerin guraren da akan iya koyan yare. Na farko shi ne iyaye (parent), na biyu shi ne abokai (friends) na uku shi ne gurin ibada (mosque and churches) na hudun shi ne makaranta (school).

Hakan na nufin: idan iyayenka sun iya turanci sosai to za ka fi iya turanci cikin sauki, idan abokanka sun iya turanci to za ka fi iya turanci, idan a wajen ibadarka ana yin ibada da Turanci to za ka fi iya turanci, sannan idan ka tafi makarantar da ana yin turanci za ka fi iya turanci.

Mu dawo kan nau’in linguistic intelligence wanda ke ba wa mutum saukin koyan yare. A kaddara ma na fi ka iya Turanci kila kai kuma ka fini iya Fulatanci kuma kamar yadda Turanci ya ke ba Yarena ba kila haka kai ma Fulatanci ya ke ba Yarenka ba. Zan iya finka fahimtar Turanci, kai kuma ka fi ni fahimtar Larabci. Don na fi ka iya Turanci hakan ma ba ya nufin na fi ka Linguistic Intelligence tun da kai ma kila ka fi ni iya wani yaren.

Wani bincike ma ya nuna wanda su ke highly intelligent suna wahalar koyon yare fiye da sauran wadanda ba su kai su fasaha ba. Binciken ya ce saboda wata cuta da ke cikin kwakwalwar mafi yawan wadanda su ke da tsananin fasaha da ake kira da ‘Dyslexia’.

Ita dai Dyslexia cuta ce ta kwakwalwa wadda ke shafar bangaren da kwakwalwa ke koyon yare, an kiyasta 10% na mutanen duniya suna da wannan cutar. Duk da Dyslexia na hana kwakwalwa kokari da saurin koyon sabon yare, amma kuma suna samun sauri da kokarin koyon abubuwan da ba yare ba cikin sauki da sauri. Misali, math ko duk abin da ya shafi ilimin science.

Saboda haka, ka da don wani ya fi ka iya Turanci hakan ya sa ka ji kamar ya fi ka basira ne. Babu basirar da ya fi ka, yanayi ne kawai ya sa ya fi ka iyawa. A wajen communication ne kawai ka ke bukatar Turanci saboda shi ne yaren da aka fi magana da shi a duniya. Amma a wajen kere-kere, likitanci, kimiya da fasaha, lissafi, tsaro, kasuwanci, iya sarrafa kudi, kwarewa akan wani aiki duka ba ka bukatar sai ka iya Turanci.

See also  HALAYE 8 DA ZASU KAIKA ZUWA GA SAMUN NASARA

English

WHY SPEAKING ENGLISH DOESN’T DETERMINE INTELLIGENCE

As I reflect on my ability to speak English fluently, I am reminded that language proficiency does not define one’s intelligence. English, like any other language, is simply a tool for communication, just as a paintbrush is to an artist or a stethoscope is to a doctor.

Growing up as a Bahaushe, I never had to attend school to learn Hausa, my native language. Similarly, one’s mastery of English does not necessarily reflect their intellectual capacity. In fact, one’s native language may be superior to that of someone who learned the language in school.

While fluency in English is commendable, let us not forget that being able to learn a second language is also a sign of intelligence. It falls under the category of “Linguistic Intelligence,” one of the eight types of intelligence, which also includes logical-mathematical, spatial, musical, bodily-kinesthetic, interpersonal, intrapersonal, and naturalistic intelligence.

However, linguistic intelligence is not the only type of intelligence that matters. In fact, it is often the weakest as it only shows one’s ability to learn a language, while other types of intelligence have made remarkable advancements in fields such as medicine, science, and technology.

It baffles me when people underestimate those who cannot speak English fluently. In Nigeria, one’s proficiency in English is often influenced by factors such as upbringing, education, and field of study. Attending an English-speaking school from birth may make one fluent in English, but to excel in subjects like mathematics, intelligence is required.

English proficiency should not be the sole basis for measuring intelligence. A British-born person may speak English fluently without attending school, but that does not mean they are intelligent in all aspects of life. Even in Nigeria, students with incomplete credentials are often sent to language learning departments, indicating that linguistic intelligence is not always a strong suit.

The ability to speak English fluently may also depend on location and religion. English is more commonly spoken in the south of Nigeria, making it easier to learn, while in the north, it is less spoken, making it more challenging. Similarly, Christians may have an advantage in learning English as the Bible is predominantly in English, whereas Muslims may have an easier time learning Arabic due to their religious studies.

While linguistic intelligence makes it easier to learn a language, it is not the only measure of intelligence. A neurological disorder called dyslexia can make language learning difficult for highly intelligent individuals, but they may excel in other areas such as math or science.

Let us not view language proficiency as a measure of intelligence. There is no superior talent, only different circumstances that favor certain skills. While English is the most spoken language globally, fluency in English is not necessary for success in fields such as creativity, medicine, science and technology, mathematics, security, business, financial management, and job experience.

See also  BOLA AHMAD TUNUBU CAPITALIST NE (PART TWO)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button