Tarihin Nana Khadijah bint Khuwaylid

Wafatin Nana Khadijah bint Khuwaylid 10 Ga Watan Ramadan Kashi Na Biyu

Ya’ya

A cewar Ruwayoyi, Annabi Muhammad (SAW) da Khadija (AS) suna da ‘ya’ya bakwai ko takwas, ko kuma kamar yadda wasu Ruwayoyi suka ce ‘ya’ya shida ne. Kamar yadda Ibn Kathir ya ruwaito daga Ibn Ishaq da Ibn Hisham, sun haifi ‘ya’ya bakwai; duk ‘ya’yan Annabi (SAW) daga ne Khadija (AS) Banda Ibrahim. Ya kawo sunayen Ya’ya shida. Kamar yadda Ibn al-Athir ya ruwaito daga al-Zubair bint. Bakkar, al-Tayyib. Har ila yau, wasu Ruwayoyi sun ambato dukkan ‘ya’yan Annabi daga Khadija (AS) ne in ban da Ibrahim. Ibn al-Athir al-Jazari Ya karbo daga al-Zubayr bint Bakkar, sunayen ‘ya’ya takwas na Annabi Muhammad (SAW) da Khadija al-Kubra.

Da alama wasu masana tarihi sun rikitar da sunaye da lakabin yara, don haka Aka Sami bambancin ƙidayar. Don haka, sun haifi ‘ya’ya shida, ciki har da ‘ya’ya maza biyu, al-Qasim da Abdullahi (al-Tayyib da al-Tahir a matsayin ‘Abd Allah’s titles) da ‘ya’ya mata hudu, ( Zainab, Ruqayya, Umm Kulthum, da Fatima (AS)

Wasu malaman tarihi sun yi imanin cewa Uwargida Fatima (AS) ita ce Kawai diyar Annabi Muhammad (SAW) Da Khadija (AS) sauran ‘ya’yan matan kuma dauko Akayi.

Musulunta

Yawancin Ruwayoyin tarihi sun dauki Khadija (AS) a matsayin wacce ta fara musulunta. Ko da kuwa wasu majiyoyi sun yi Wani iƙirarin, an yarda da Wannan a tsakanin duk masu bincike. Ibn Abd al-Barr yace Ali ibn Abi Talib (RA) shi ne farkon wanda ya musulunta bayan Khadija. Ruwayoyi da suka yi magana game da lokacin sahaba wajen musulunta sun ambaci Khadija al-Kubra da Ali ibn Abi Talib (RA) a matsayin mutum na biyu dana farko da suka musulunta. Sun bayyana cewa su ne mutane biyu na farko da suka yi sallah tare da Annabi Muhammad (SAW).

See also  Nana Khadijah, (RTA) matar manzon Allah (SAW) Wadda Matan Zamani Za Su Yi Koyi Da Ita Wajen Dogaro Da Kai

Matsayi A musulunci

Bayan taimakon kudi daga Khadija al-Kubra, Annabi Muhammad (SAW) ya samu gata ta kudi. Kamar yadda Allah ya ambaci baiwar da aka yi wa Annabi Muhammad (SAW) cewa: “Allah ya same ku mabukata, kuma ya wadata ku.” Har ila yau, Annabi Muhammad (SAW) yana cewa: “Babu wani kudi da ya amfana min kamar dukiyar Khadija. Annabi Muhammad (SAW) ya yi amfani da dukiyarta wajen biyan basussukan masu binsa bashi, da Taimakawa marayu da talakawa.

Lokacin da mutanen Makka suka kauracewa Banu Hashim, dukiyar Khadija al-Kubra ta taimaka wa Banu Hashim. Kamar yadda wata ruwaya ta ce: “Abu Talib da Khadija sun sadaukar da dukiyoyinsu domin kare Musulunci da kuma taimakon musulmin da aka kauracewa”. Hakim ibn Hizam dan uwan ​​Khadija ya kawo dabino, da ‘ya’yan itatuwa, da alkama da wahala kuma cikin yanayi mai hadari ga Banu Hashim. Irin wannan sadaukarwa da karamci na Khadija Allah ya karbe shi kuma ya dauke shi a matsayin kyauta ga Annabi Muhammad (SAW). Annabi ya kasance yana ambaton sadaukarwarta kuma yana godiya ga karamcinta.

Khadija (AS) ta kasance fitacciyar mace, abin dogaro, kuma hamshakin attajiri a zamaninta. Jabir ibn. Abdullah al-Ansari ya ruwaito hadisi daga Annabi Muhammad (SAW) wanda ya ambaci mafifitan mataye: Khadija (AS), Fatima (AS) 3, Maryama (Mahaifiyar Annabi Isa AS) da Asiya (Matar Fir’auna) Bugu da ƙari, Annabi ya kira ta a matsayin ɗaya daga cikin cikakkun matan duniya da kuma ɗaya daga cikin mafi kyawun mata. Kamar yadda aka ruwaito ana kiranta da suna al-Tahira (mace tsarkakakkiya), Zakiyya (mace mara laifi), al-Marziyya (mace mai daraja), al-Sidiqqa (mace mai gaskiya), Kuma babbar mace ta kuraishawa. Umm Hind, Umm al-Zahra, da Umm al-Mu’minun Wannan sune sunaye na kunyarta.

See also  Wafatin Nana Khadijah bint Khuwaylid 10 Ga Watan Ramadan Na Uku (3) Kuma Na Karshe

Kamar yadda bayanai suka nuna, Khadija (AS) ita ce mafificiya kuma mafi gaskiya Ga sahabbai kuma mashawarciyar Annabi Muhammad (SAW). Khadija al-Kubra (AS) tana da matsayi mai girma a mahangar Annabi Muhammad (SAW) An bayar da rahotanni da dama kan irin rawar da Khadija ta taka a rayuwar Manzon Allah, ta yadda bayan wafatinta shekaru da yawa, Annabi (SAW) ya kasance yana tunawa da ita a matsayi na musamman a rayuwarsa.

Khadija ta kasance mace mai ilimi da daraja. Kamar yadda Ibn al-Jawzi ya ce: Khadija ta shahara da ilimi, adalci, ci gaba, da sha’awar Addini da kamala. Tun tana karama ta kasance mace mai daraja da kirki a cikin Larabawa a Hijaz. Arzikinta marar iyaka Amma Addini ya fi girma fiye da dukiyarta mai ban sha’awa.

Duk da cewa manyan mutane kuma attajiran Kuraishawa daban-daban sun nemi auren Khadija amma ta ki su. Ta zabi Muhammad (SAW) Ita ce mace ta farko da ta musulunta, ta karbi annabcinsa kuma ta yi salla tare da Manzon Allah (saww).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button