Yadda Zaka Tinkari Mace Ba Tare Da Ta Zulle Maka Ba
#Tsangayarmalamtonga
Maza da dama suna son tinkara mata domin neman aurensu amma kuma sukan ji shakku ko tsoron matan na iya bagarar dasu. Ga wasu dabarun tinkaran duk wata mace ba tare da race A’a ba.
1: Kayi kokarin Saninta: Mata basu cika daukan mazan da suka ce suna sonsu a ranar da suka gansu ba da mahimmanci. Don haka kamin ka cewa mace kana sonata ka tabbatar da kana da wasu bayanai akanta.
Misali kasan sunanta, inda take karatu ko aiki, suna wani makusancinta. Da kuma abunda take so ko tafi so. Da wannan ne zaka mata tarkon farko.
Kana kiran sunanta tana waigowa idan kace mata daman kana so ka tambayeta akan wani da kasani na tare da ita ka fadi sunansa ko kuma akan karatun ko aiki zata tsaya kuma ta saki jiki.
2: Lokaci Mafi Dacewa: Kada kace zaka yiwa mace magana a lokacinda batada lokacin baka lokaci.
Ka kula da yanayin ko tana da wani uzuri ko tana sauri ko tana tare da wasu mahimman mutanen da bazata so magana da kai ba a wannan lokacin.
Kana neman natsuwanta ne da lokacin ta. Don haka ka tabbatar kamin kayiwa mace magana sai ka fahimci tana da lokacin da zata saurareka.
Rashin la’akari da hakan ne wasu mazan suke zargin wasu matan da wulakanci amma a zahiri sune basu tinkaresu a lokacin da ya dace ba.
3: Ka Tinkareta Kai Tsaye: Duk wata mace bata son namiji ya zo yana mata nuku nuku ko rawan baki a lokacinda zai mata magana.
Duk matsayin mace ka kalli cikin idanuwanta cikin mazantaka hade da murmushi ka fadamata abunda yakawoka gareta.
Da zaran mace taga kana tsoro ko shakku yi mata magana ko ka daburce, daga wannan lokacin zaka iya rasa soyayyar ta suna son idan sun hadu dana miji ya nuna musu shi namiji ne.
4: Kada Ka Ja Zancen Da Tsawo: Ganin haduwarku ko tsayuwarku na farko kenan. Kada ka. Bata mata lokacin da dogon bayanai ko surutai koda kuwa tana da lokacin saurarenka.
Ka tabbatar ka soma gabatar da kanka yadda zaka dauke hankalinta. Idan kayi shiga mai kyau da tsada kada kace mata kai wani mai kudi ne ko attajiri, idan kuma kwalliyar ka ba mai tsada bane kada ka nuna mata ka fa matsiyaci ne. A’a, mace bata son mai yawan alfahari kuma bata son fakiri mara abun yi.
5: Ka Saurareta: Akwai yiwuwar ta maka wasu tambayoyin kada kaji nauyin amsa matasu. Haka nan idan tana magana kada ka katsaita.
Ka tabbatar wajen mata bayanin abunda yasa kake sonta ka zuga ta sosai. Daga karshe ka kirkiro wani maganar da zata son ka karashi amma ka nemi ta baka lokaci domin mata wannan bayanin ko bata wannan labarin.
Ka Jaraba wannan da sauran dabadurun da muka koyar a darusan mu na baya domin tinkaran macen da ka gani kana so.
Muna godiya da waazi,amma munaso ku kawo mana kalaman soyeyya masu ratsa zuciya.