EducationTech

Duniyar Metaverse, Web-3 da Blockchain za su share wa TikTok hawaye

Duniyar Metaverse, Web-3 da Blockchain za su share wa TikTok hawaye

Duba da yawan yadda gwamnatocin duniya suke ɗaukar dokar haramta TikTok a ƙasashensu, tun daga kan Pakistan, Bangladesh, Indonesia, Iran, Taiwan, Canada, Jordan da sauransu, a yanzu kamfanin yana ƙoƙarin nema wa kansa mafita.

Haka nan dai su ma US da EU suna duba yiwuwar haramta shi, wannan ya kara zaburar da kamfanin yin abun da ya dace don nema wa kansu mafita.

Duk da TikTok bai jima a duniya ba, amma ana yawan samun cece-kuce a kansa inda manyan ƙasashe suke kulle shi, sannan wasu ƙasashe da dama suna barazanar rufe shi.

Tun lokacin da aka hana Twitter a Nigeria manyan kamfanonin duniya suke naman hanyar da za su kuɓuta daga irin wannan banning ɗin, musamman ma shi Twitter ɗin.

A yanzu TikTok da sauran kamfanonin fasaha suna ƙoƙarin samar da yadda za su kuɓuta daga gwamnatocin da suke haramta su a ƙasashensu, ta yadda za a samar da yadda za a yi kowa ya iya amfani da su ko da an haramta.

Duniyar metaverse za ta share wa duk waɗannan kamfanonin hawaye, wacce ita ce ta ƙunshi fasahohi kala-kala a ƙarƙashinta, kamar su AI, VR, AR da sauransu. Haka nan dai saboda cigaban fasahar blockchain da kuma next version na internet wato Web-3.

Duk da mutane suna amfani da VPN lokacin da aka haramta Twitter, to idan aka yi nasarar ɗaura waɗannan apps/websites ɗin a decentralized network ba za a iya hana mutane shigarsu kai-tsaye ba kamar yadda aka saba yi.

Duk da cewa har yanzu akwai dokar hana kasuwancin cryptocurrency a Nigeria, amma babu abun da ya canja saboda akwai exchange wallets da dama waɗanda ba za a iya hana su yin transactions ba, saboda ba direct da Naira ake yi ba.

To kamar haka ne, ba abu ba ne mai sauƙi, ko kuma in ce kai-tsaye ba zai yiwu a hana TikTok ko wani app a duniya ba matuƙar ya hau decentralized network, saboda su ma za su kawo premium VPN wanda gwamnati ba za ta yi interfering a ciki ba.

Idan gwamnati ta dogara da ISPs na ƙasar kamar su MTN/Airtel, a yanzu an samu cigaban amfani da home/mobile Wi-Fi irin Starlink wanda shi kuma server ɗinsa take sararin samaniya.

Idan sai Starlink ya nemi izini kafin ya yi operating a wata ƙasa, waɗannan kamfanonin a shirye suke don samar da service irin Starlink wanda ba ya buƙatar izinin kowacce ƙasa kafin ya shige ta, kuma za a ba wa kowa izinin subscribing da connecting direct daga wayarsa duk inda yake ba tare da amfani da hardware devices ɗin ba.

Wannan banning ɗin da ake musu yana matuƙar ci musu tuwo a ƙwarya, kuma a shirye suke duk yadda za su yi su shawo kan matsalar.

Duk da TikTok ya san cewa ba komai ba ne yake sa ake rufe shi sai batun data privacy da indecency, amma ya ce yana bakin ƙoƙarinsa wajen hana high-level na indecency ɗin. Ita kuma US daman siyasa ce ya sa take barazanar rufe TikTok a ƙasarta, duk da cewa headquarter ɗin TikTok yana US ɗin.

A yanzu haka duniya ta farga, kowanne kamfani yana fafutuka a duniyar AI, to haka nan kowanne kamfani zai farga ya shiga duniyar metaverse da blockchain nan da shekaru kaɗan, saboda sanin cewa AI zai taka muhimmayar rawa a waɗannan duniyoyin.

Duk binciken da duniyar kimiyya da fasaha yanzu suna yi ne saboda gobe, wato tanadin gobe ake yi, ana ta shirya yadda duniya za ta ci gaba zuwa gobe. Wannan shi ne bambancin Bature da mu.

—Muhammad Auwal Ahmad (#Mohiddeen)
13th March 2023

See also  BANBANCI TSAKANIN MTN "SME DATA" DA KUMA "DIRECT DATA"

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button