Nasiha

Fa’idodin karanta Suratul Al-Imran



Surar Al-Imran, surar Madaniya ce ta na da Kyau a karanta ta ranar Juma’a, Haka kuma ana kyautata zaton cewa duk wanda ya karanta wannan sura tare da Suratul Baqarah, a ranar kiyama za a ba shi kariya da gajimare Saboda zafin ranar.

A cikin wannan sura akwai jimlar ayoyi 200 kuma ta sauka a Madina. Manzon Allah (SAW) ya ce duk wanda ya karanta suratul Ali-Imran a ranar Juma’a, har zuwa faduwar rana, Allah zai yi masa rahama Allah kuma Mala’iku suna nema gafara.

1, Masoyinmu Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce wa Muaz (RadiAllahu anhu):”Shin, ba zan sanar da ku wata addu’a wadda idan kum kasance kuna roƙon Allah Da Ita Allah Ya Zai Biya muku Dukkan bashin da Ake ku, ko da girmansa kamar Dutsen Uhudu?” Sannan ya ambace ta (watau suratu al-Imran aya ta 26 & 27)‛ [Tabarani a cikin Al Saghir 1/330].

2, Abdullahi bn Mas’ud (RA) ya ce: “Madalla da suratu al Imrana maganin matalauci idan Mutum ya karanta ta a cikin addu’a a cikin karshen dare”.

3, Masoyinmu Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: ”Mafi girman sunayen Allah, wanda idan aka kasance ana rokonsa sai ya amsa, yana cikin surori guda uku. Al Baqara, Al’Imran, da Taha’ [Hakim & Ibn Majah 3856].

Babban Jigon Suratul Al-Imran:

Babban jigon wannan sura ta farko shi ne Shiriya. Tana kira ga dukkan mutane zuwa ga addini, kuma tana ba su labarin ladan da za a bayar a Cikin hukunce-hukuncen sa.

Babban jigo na biyu na wannan sura shine game da kadaita Allah. Allah shi ne mahalicci don haka shi ne kadai abin bautawa.

Tsayawa akan gaskiya shine jigo na uku. Tana dauke da Addu’a a cikin Farkon budewa wato:

“YA UBANGIJINMU! KADA KA KARKATAR DA ZUKATANMU A BAYAN KA SHIRYAR DA MU, KUMA KA BA MU WATA RAHAMA DAGA WURINKA. LALLAI KAI NE MAI BAYARWA.” (3:8)

Masu Neman Aure Mata Da Maza

A Karanta suratul Ali-Imran Kullum Kwana 21 In shaa Allahu za’a ku Sami Aure Mai Albarka cikin wa’adin Kwanaki 21 Amma ku tabbatar da kun cika wannan Wazifa na tsawon kwana 21 ko da kun Samu kunyi auren kafin wa’adin.

Ya Allah Ya Bamu Albarkacin Alkur’ani Amen ????

See also  Tausayin Annabi Ga Dabbobi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button