A yayin da wasu matan suke kokawa wajen bushewar gabansu saboda rashin ni’ima, wasu kuma damunsu yake da zuba ba kaukautawa.
Hakan yasa mata masu irin wannan baiwa suke shiga damuwa saboda yadda a kullum suke jika kamfensu ko kullum suna cikin kunzugu ko suna al’ada ko basu yi.
Shi dai zubar ruwan gaban mace ba yana nufin mace na dauke da wata cuta bace, shi wannan ruwa asali ma yana kare mace daga kamuwa daga cututtuka dake shiga farjin mace.
Haka kuma ruwa ne dake bada damar azzakari ya shiga farji cikin sauƙi ba tare da cutar da gaban mace ba. Haka kuma yana karawa mace daɗi jima’i wanda idan ba namijin gaske ba yana da matukar wahala namiji ya iya jimawa akan macen mai wannan ni’imar bai yi zuwan kai da wuri ba.
Don haka wannan ruwa ne da kowace mace zata yi burin ganin tana da shi. Sai dai kuma yawan sa da har zai rika jika suturan mace yakan saka mata cikin Damuwa.
Wannan matsalar yafi damun matan da basu da aure saboda rashin samun yin jima’i. Matan masu aure ma da basu samun yin jima’i kamar yadda ya kamata suma suna iya fama da irin wannan yanayin.
Akwai hanyoyin na yanayin da ba sai mace ta sha magani ba zata iya rage Zuban ni’iman kuma bazata cutu ba.
shi wannan ruwan dake zubowa daga gaban mace yana da matukar amfani ga mata ganin yadda yake fitar da duk wata dauɗar da bai kamata ya zauna a gaban mace ba.
Duk da haka akwai kuma yanayin da wannan zubar ruwan na iya zama na wani cuta ne da mace ta kamu dashi. Don haka yana da matukar kyau mace ta kula da irin ruwan dake fita daga gabanta domin iya tantancewa.
Kamin mu kawo yadda mace zata iya rage zubar ruwan gabanta, yana ya kamata ta iya fahimtar irin ruwan dake iya zama na cuta ne domin ganin likita.
Da akwai nauyinkan zuban ruwa kala kala ga mata har guda biyar. Wanda dukkaninsu suna bukatar kulawa ko ganin likita.
1: Farin Ruwa Mai Kauri- shi wannan ruwan yana yawan fita a gaban mace ne kwanaki kadan kamin yin al’ada da kuma bayan kammala al’adar mace.
Sai dai da zaran wannan ruwan yana fitowa mace sai tana jin kaikayi a gabanta, ko kuma gaban nata yana kumbura, to akwai matsala ya kamata ta ga likita.
2: Ruwan Kwai- Da zaran mace taga tana zubar da ruwa a gabanta mai launin ruwan kwai, To da matsala. Ko dai wasu kwayoyin Cututtuka sun shige ta ko kuma ta kamu da wani cutar da hanyar jima’i.
3: Ruwan Ƙasa- Idan mace taga tana fidda ruwa a gabanta mai launin ƙasa-ƙasa ta akwai matsala.
Shi wannan matsalar yana aukuwa ne a Sanadiyar birkicewar lokutan al’adar mace. Ko kuma cutar mafitsara. Don haka da zaran mace taga irin wannan ruwa ta garzaya likita.
4 : Ruwan Gaye-Shima alama ce ta mace tana dauke da cutar da ake kamuwa ta hanyar jima’i don haka ganin likita ya kamata.
5: Yeast- A turance yeast discharge yana afkuwa ne a lokacin da mace tayi sakaci har cutar zuban ruwa ya ci karfin ta. Yakan kumburan da gaban mace, yana mata mugun kaikayi zata rika fitar da wani farin ruwa mai Warin tsiya.
Waɗannan sune fitar ruwa a gaban mata da akasarin mata suke fama da guda daga cikinsu. Wanda na farkon nan ne kadai baya dauke da matsala wanda kuma shine muke magana a kansa. Wanda a darasin mu na gaba zamu kawo yadda mace zata iya rage zuban wannan ruwa mara dauke da wani cuta.
Zamu ci gaba……