Jima'i

Yadda Zaki Gamsar Da Mijinki



Gamsar da namiji a jima’ince yafi sauki wajen gamsar da mace, duk kuwa da cewa dukkannin halittan da aka yiwa mace a jima’ince suma maza suna da irinsa.

Kamar yadda ake samun harijin namiji haka nan ma ake samu harijan mace, yadda ake samu mazan da suke jimawa babu gajiya a lokacin jima’i hakama matan.

Ana samun maza da mata ragwaye a wajen jima’i da kuma wadanda sam jima’in ma bata damesu ba a dukkannin jinsunan biyu.

Da akwai wasu mazan da basu cika son doguwar wasannin motsa sha’awa ba, wasu kuwa suna bukatan lokaci maitsawo ana masu wasa duk kuwa da
macen tafi namiji bukatar wasan motsa sha’awa mai tsawo.


Abu na farko daya kamata mace ta fahimta a tattare da mijinta shine abunda yafi bukata a yayi wasannin motsa sha’awa da kuma lokacin kwanciya irin na jima’i, domin da akwai inda da zaran mace ta tabawa mijinta maimakon ta motsa mishi sha’awarsa sai kawai sha’awar tashi ya gushe. Hakama a kwanciyar jima’i, yana da kyau ki fahimci irin yanayin kwanciyar da mijinki yake so.

Shi yasa malamai na jima’i suke cewa sadarwa a jima’i yanada matukar alfanu ga ma’aurata domin ta hanyarce
zasu iya fihimtar abubuwan da suke bukata a yi musu kamin, lokaci da kuma bayan jima’i.

Da akwai mazan da zaran mace ta fara wasa dasu nan da nan suke gamsuwa ba tareda sun shegetaba, da akwai wadanda da zaran azzakarinsu ya shiga shikenen kuma sunyi zuwan kai kenan.

A akwai mazan da sukan
dauki lokacin mai tsawo suna jima’i da mace kamin suyi zuwan kai, wasu mazan kuwa a lokacin da suke kawowa a lokacin ne gabansu ke kara yin karfi har sai sun kawo sama da biyu koma biyar kamin suke gamsuwa da
mace. Ke naki mijin yaya yake? , domin dole sai kin fahimci yadda yake kamin ki iya gamsar dashi.

See also  Dalilan Da Suke Hana Wasu Matan Sha'awar Jima'i


Sai dai maza masu wuyan sha’ani a jerin mazan da na ambata sune masu saurin zuwan kai da kuma masu daukan lokaci mai tsawo suna gurza mace basu gamsu ba, sai dai kuma da zaran mace ta samun illimin sarrafa irin wadannan maza ta gama dasu.

Maza masu saurin zuwan kai sune mazan da sukafi cutar da matansu, domin wata matan sai ta gurzu take gamsuwa, don haka matsalar irrin wannan mazan yana tattare ne da kodai suna da cuta da suke bukatar ganin likita, ko kuma sabbin shiga ne wato mazan da suka yi aure sabo-sabo ko waɗanda suka jima basu yi jima’i ba.


Sai dai kamin mu fara kawo muku cikenken wannan darasin. Zai fi kyau mu fara hanyoyin da zaki motsawa mijinki sha’awa cikin sauƙi. Domin muddin namiji bai dai sha’awar jima’i dake babu yadda za ayi kuyi ma jima’i bare kuma ki gamsar dashi.

Don haka mataki na farko shi ne kokarin fahimtar hanyoyin da mace zata iya motsawa mijinta sha’awar sa cikin sauƙi. Wanda a darasi na gaba da shi zamu fara.


Sai dai kuma darusa ne da dole sai anyi amfani da kalmomi na motsa sha’awa da kuma kalamai da ba kasafai ake faɗin su a fili ba. Ganin kuma wannan shafi shafine da masu aure da marashi suke bibiyan darusan mu.

Muka ga ya kamata mu nemi shawaran dalibai da masu karatu ko mu ci gaba da gudanar da wadannan darusa a bayyane ko kuma mu keɓe masu aure mu karantar dasu. Muna son jin ra’ayoyin ku.

See also  Abubuwa 10 Dake Tayarwa Mata Sha'awa Ba Tare Da An Kusancesu Ba

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button