Jamb
Trending

Abubuwan Da Yamata Ku Yi, Bayan Rijistar JAMB

• Babban abinda ya kamata ku durfafa, da zarar kun kammala rijistar jarrabawarku ta JAMB shi ne, dagewa da karatu. Kuma, ba wai muna nufin ku yi karatu ba tare da wani kyakykyawan tsari ba, a’a zai fi kyau ku yi karatun ta hanyar amfani da JAMB Syllabus (Wanda kundi ne da ke ɗauke da jerin wuraren da hukumar JAMB za ta yi tambayoyinta, a kowanne Subject), idan so samu ne ma, ya na da kyau ku karance dukkannin Topics ɗin da su ke cikinsa (Covering).

•Ya na da kyau ku ma, ku waiwayi tambayoyin da JAMB ta yi a shekarun baya (Past Questions), saboda hukumar tana dawo da tambayoyinta na shekarun baya, baya ga haka, duba su ɗin zai sanya ku fahimci yadda hukumar ta ke tsara tambayoyinta.

• Ku karanta Littafin ‘The Life Changer’, da aka damƙa muku, a wurin rijista (idan ya yi mu ku tsawo ku nemi Summary ɗinsa), sannan ku duba ire-iren tambayoyin da ka iya fitowa daga cikinsa, da ma amsoshin su (Possible Questions & Answers).

• Ka da ku yi shiru da bakinku idan kuna da wasu tambayoyi. Ku yi wa ASOF tambayoyin ku, game da dukkannin abubuwan da su ka shige mu ku duhu, kan makarantar da ku ka zaɓa, ko dukkannin wani abu da ya shafi jarrabawar ku. Mu kuma zamu amsa muku tambayoyin a cikin ƴan mintuna (Insha’Allah!).

•Ku cigaba da bibiyar Labarai (a shafin ASOF), dan sanin halin da ake ciki game da Re-Printing, da ma lokacin rubuta jarrabawar.

Samun maki 300+ a JAMB abu ne mai sauƙi, muddin za ku mayar da hankali akan karatu, ba tare da duban dogon lokacin da ake da shi kafin rubuta jarrabawar, da ma yarda da cewar ”JAMB SA A CE” ba.

See also  Cikakken Tarihin hukumar Jamb

Alƙalamin✍️ : Miftahu Ahmad Panda

   08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button