LawMukoyi shari'aShehu Rahinat Na'Allah

Shin a doka zan iya yawo da Makami don kare kaina ?

Marubuci: Shehu Rahinat Na’Allah

Na farko dai, shi “Kare kai” ko “Self-defence” ko kuma “Se defendendo” wani term ne a Law da aka samo shi daga Yaren Latin, kuma duk duniya kowace ƙasa ta yarda dashi, ta amince duk lokacin da wani yayi yunƙurin kashe ka, ko taɓa lafiyar ka, ko ƙwace maka dukiya to an yarda ka kare kanka da duk abinda zaka iya kare kanka dashi, sannan a wurin kare kan nan naka koda ka kashe (shi wanda yazo ya ƙwace maka dukiyar ka, ko wanda yazo kashe ka, ko taɓa lafiyar ka) to babu abinda doka za tayi dakai, kamar yadda yazo a cikin Constitution, domin samun cikakken bayani akan Self-defence Shiga nan:
https://www.facebook.com/100005616875393/posts/1802706763259869/?app=fbl

To mu koma kan maganar mallakar Makami da kuma yawo dashi.
Idan muka duba za muga an raba makami zuwa gida biyu kamar haka:

1• Firearms:
Daga cikin Firearms akwai irin su Bindiga Pistol, AK-47 da Ire-iren su, kuma haramun ne mutum ya mallake su bare ma har yayi yawo dasu ba tare da hukuma ta bashi izinin yin haka ba, don haka duk wanda yake so ya mallake su har ma ya riƙa yawo dasu, to dole sai ya nemi Sahalewar Shugaban ƙasa ko Shugaban Rundunar Yan Sanda na ƙasa ta hannun wakilan su, domin samun Cikakken bayani akan wannan, to shiga nan:

Me doka tace akan Civilian dinda ya kashe Dan ta’adda wajen Kare Kanshi


2• Offensive Weapons:
Offensive Weapons sun haɗar da: Wuƙa, adda, Gatari, Gariyo Barandami, almakashi, da Makamantansu, to su waɗannan babu wata dokar Nigeria da tace ta haramta maka mallakar su bare kuma yawo dasu, abinda dokar ƙasa ta haramta maka Shine kayi amfani dasu wajen aikata laifi, kazalika babu wata doka da tace dole sai ka nemi izinin Jami’an tsaro ko shugaban ƙasa idan kana so ka mallake su, don haka zaka iya mallakar abinka kuma zaka iya yawo dasu, domin kuwa Sashi na 8 na Public Order Act cewa yayi haramun ne ka shiga dasu a cikin inda mutane suke taro, ko wurin hada-hadar su, kenan kunga in ba anan bane babu laifi, to amma inda matsalar take shine idan har aka kama ka da irin waɗannan Offensive Weapons din a tare dakai ta yaya za’a gane cewa ba wai kana yawo dasu bane don ka aikata laifi ba, ta yaya za’a gane cewa kana yawo dasu ne don kare kanka ? Ta yaya zaka gamsar da Jami’an tsaro da kuma al’umma ? Saboda ba fa rubuce yake a goshin ka ba bare kace ai kowa zai gani, don haka nidai a fahimta na duk da doka batace haramun ne a ganka dasu ba, to amma gwara kawai mutum ya haƙura saboda Safety, don ina tabbatar maka idan har aka samu akasi Jami’an tsaro suka ganka kana yawo dasu to ba kada wata Shaidar da zata tabbatar masu cewa ba kana yawo dasu bane don ka aikata wani laifi ba, a ƙarshe kuma sai kuga mutum ya tsinci kanshi cikin wata masifar ta daban, Allah ya kyauta. Amma da ace ana bada lasisin riƙe ta ne da Shikenan sai duk mai bukatar yawo da ita sai yaje ya nema lasisin.

My Statutes:
1• CFRN
2• Public Order Act
3• Criminal Code
4• Firearms Act
5• Robbery and Firearms Act

Bissalam

See also  Idan naje Cire kuɗi sai suka Maƙale a POS ko ATM ko ONLINE zan iya zuwa kotu neman diyya ?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button